Header Ads

Yadda rakiyar da Gwamna Kano ya yi wa tagwayen da ke manne da juna zuwa filin jirgi ta ɗauki hankalin Kanawa da ƙasa baki ɗaya

Gwamna Abba Yusuf Kabir na Kano rike da jariran da suke manne sa'ilin da za su bar filin jirgin saman Malam Aminu Kano zuwa Saudiyya don yi musu aikin raba su.


Makonni biyu bayan Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya raka ɗalibai masu tafiya karatu ƙasashen waje har zuwa cikin jirgi domin ya ga tashin su, gwamnan wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, ya sake komawa filin Jirgin Malam Aminu Kano, a wannan karo domin yin rakiya ga tagwayen da aka haifa manne da juna, waɗanda za a yi wa aikin tiyatar raba su a Saudiyya.
Tuni dai tagwayen sun isa Saudiyya, a nan gida Kano da Najeriya kuma sai yabon gwamnan na Kano ake yi.

Kwana ɗaya kafin rakiyar tagwayen a filin jirgin sama, Abba ya je wani asibiti inda aka nuno shi ya na raba wa majiyyata kuɗaɗen da likitoci su ka nema kafin a yi masu aikin da ya zama tilas a yi masu.
An kuma nuno shi ya na rungume da wata ƙaramar yarinya, wadda aka watsa hoton ta a soshiyal midiya, bayan mahaifiyar ta ta ce mata ta tashi su tafi gida, domin ita mahaifiyar ba ta da kuɗin da likitocin su ka nema kafin a yi wa yarinyar aiki a ƙafar ta, wadda aka nuno a kumbure.

Gwamnan Kano
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yaba wa gwamnatin Saudiyya kan ɗaukar nauyin yin tiyatar raba tagwayen da aka haifa manne da juna a jihar.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai, Sanusi Bature ya fitar, an ruwairo Gwamna Abba ya yi wa tagwayen da iyayensu rakiya zuwa Filin Jiragen Sama na Malam Aminu da ke Kano, inda suka tashi zuwa birnin Riyadh na Saudiyya da za a yi musu aiki a can a ranar Litinin.
A yayin rakiyar tasu, gwaman ya gode wa Sarki Salman na Saudiyya a kan wannan ƙoƙarin, tare da addu’ar Allah Ya biya shi.

Gwamnan ya kuma tuno da yadda ba a daɗe ba da wasu likitocin ƙasar Saudiyyar suka je Asibitin Koyarwa na Aminu Kano suka yi wa masu fama da ciwon zuciya da na idanu aiki a kyauta.

Ya yi wa jariran fatan a yi musu tiyata cikin nasara su koma koma gida lafiya a matsayin lafiyayyu.

Da yake nasa jawabin, babban jami’in Ƙaramin Ofishin Jakadancin Saudiyya a Kano Shiekh Khalil Al’adamawi, ya bayyana cewa irin wannan shiri yana nuna ƙoƙarin da Saudiyya ke yi wajen kyautata jinkan al’umma da kuma sadaukarwa ga mabuƙata.

Da ke godiya, mahaifin mannannun tagwayen mai suna Isa Hassan, ya gode wa Sarki Salman bin Abdul'aziz na Saudiyya, kuma ya gode wa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.

No comments

Powered by Blogger.