Header Ads

Taron Duniya: Minista ya sha alwashin Nijeriya za ta ɗau nauyin sabuwar makarantar UNESCO a Nijeriya

Alhaji Mohammed Idris (na 2 daga hagu); tare da Farfesa Prof Tahir Mamman (a dama); Da Darakta-Janar ta UNESCO, Miss Audrey Azoulay (ta 3 daga hagu); da sabon Shugaban Babban Taro na 42 na UNESCO, Ambasada Simona-Mirela Miculescu (a tsakiya), da Jakadiyar Nijeriya Dakta Hajo Sani (ta 3 daga dama), a Paris, ranar Talata

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana ƙudirin Gwamnatin Tarayya na buɗe babbar makarantar koyar da aikin jarida da ilimin labarai ta Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya ba tare da ɓata lokaci ba, wato 'UNESCO Category 2 Institute for Media and Information Literacy' (MIL).

Ministan ya faɗi haka ne a wajen taron ƙasa da ƙasa na Mataimakin Darakta-Janar mai kula da Yaɗa Labarai na UNESCO, Dakta Tawfik Jelassi, a wani sashe na Babban Taro na 42 na hukumar UNESCO a ranar Talata a Paris, babban birnin ƙasar Faransa.

Wannan alƙawari da Nijeriya ta yi na buɗe tare da ɗaukar nauyin makarantar, an yi shi ne tun lokacin da aka yi Makon Aikin Jarida da Yaɗa Labarai na Duniya na UNESCO na shekarar 2022, wanda aka yi a Nijeriya cikin Oktoba 2022, a Abuja, wanda kuma aka rattaba hannu kan ƙudirin sa a Zama na 216 na Babbar Hukumar Gudanarwar UNESCO, cikin Mayu 2023.

A wannan taron, wanda aka gudanar a hedikwatar UNESCO ɗin, ita ma Jakadiyar Nijeriya kuma Wakiliyar Dindindin a UNESCO, Dakta Hajo Sani, ta halarta.

Yayin da ya ke ƙara tabbatar da sadaukarwar Nijeriya ga manufofi da burukan UNESCO, Minista Idris ya bayyana cewa duk da yake ƙasar nan ta na shirin sauka daga kujerar ta a Majalisar Ƙasa da Ƙasa ta Shirin Cigaban Harkokin Yaɗa Labarai na Duniya na UNESCO (IPDC), bayan ta shafe shekaru shida a majalisar, to kuma ta na neman zama memba a Majalisar Ƙasa da Ƙasa ta Shirin Samar da Labarai ga Kowa, wato 'Information for all Programme' (IFAP).

Idris ya sha alwashin cewa zai tabbatar Nijeriya ta ci moriyar dukkan wasu damarmaki da ke akwai a Sashen Aikin Jarida da Yaɗa Labarai na UNESCO, ciki kuwa har da samar da ƙananan gidajen rediyo na unguwanni, wanda ya na daga cikin tsare-tsaren da UNESCO ta ke ba muhimmanci a yanzu.

Ya ce: “Ina farin cikin ganin cewa zuwa na Paris ya yi alfanu matuƙa, musamman wannan zaman. Wannan wani ɓangare ne wanda na ke da sha'awa sosai da sosai. 

“A ko yaushe na kan ce idan na gama aikin Minista, zan koma fagen aikin jarida ne, inda da ma a can na ke. Saboda haka haƙƙi na ne in ga na taimaka wajen inganta shi, don haka zan ba da cikakken goyon baya da haɗin kai ga UNESCO.”

Ministan ya kuma bayyana ƙudirin sa na dawo wa da kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Nijeriya mutunci da ƙimar su, tare kuma da samar da tattaunawar ƙasa gaba ɗaya kan kyawawan ɗabi'u da halayen Nijeriya, a matsayin wani shirin gangamin wayar da kan jama'a da za a yi a duk faɗin ƙasar, wanda ya ce al'amari ne da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka da muhimmanci.

Ministan ya gode wa Jakadiya Hajo Sani saboda aiki tuƙuru da ta ke yi na wakiltar burukan Nijeriya a UNESCO, da muhimmiyar rawar da ta taka wajen samar wa Nijeriya damar zama mai masaukin baƙi a Makon Aikin Jarida da Yaɗa Labarai na Duniya na UNESCO na shekarar 2022, da kuma shirye-shiryen da ake yi don ɗaukar nauyin da Nijeriya za ta yi na buɗe babbar makarantar 'UNESCO MIL Institute' ta farko a duk duniya.

Da ya ke mayar da jawabi, Mataimakin Darakta-Janar na UNESCO, Dakta Jelassi, ya yaba wa Nijeriya kan babbar rawar da ta ke takawa a UNESCO, sannan ya yi alƙawarin hukumar za ta ci gaba da mara wa ƙasar baya domin ta ci moriyar dukkan damarmakin da ke akwai na haɓaka ɓangaren ta na aikin jarida da yaɗa labarai.

Ya lissafa ayyukan da UNESCO ke aiwatarwa a sassa daban-daban, daga tabbatar da 'yancin 'yan jarida a ƙasashen duniya, zuwa tallafawa wajen kafa gidajen rediyo na unguwa, da aikin da ake yi don daidaita ayyukan da ƙasashe ke yi wajen yaƙar baza labaran bogi, da labaran ƙarya da kuma kalaman ɓatanci. 

Ya bayyana cewa UNESCO ba ta daɗe da ƙaddamar da wani rahoto ba mai suna, ‘Guidelines for the Governance of Digital Platforms’, wanda ya ɗora muhimmanci kan hanyoyin da za a bi a tsare 'yancin faɗar albarkacin baki da damar samun yaɗa labarai.

Haka kuma ya nanata buƙatar da ke akwai ta Nijeriya ta aiwatar da Ƙudirin Abuja, ya ce muhimmin abu ne ga ƙasar.

Tun da farko, mai girma Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya na cikin ayarin sauran mahalartan taron daga Nijeriya, ciki har da shugaban tafiyar, wato mai girma Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman (wanda kuma shi ne Shugaban Hukumar UNESCO ta Ƙasa), da su ka halarci bikin buɗe Babban Taro na 42 na UNESCO.

No comments

Powered by Blogger.