Header Ads

NAZARI, AIKI SAI MAI SHI: Ayyukan Raya Jiha Da Inganta Rayuwar Jama'a Fiye Da 300 A Kasafin 2024 Na Gwamnatin Namadi A Jigawa Daga Suleiman Aliyu

Ga dukkan mai bibiyar salon mulkin Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa tun daga farkon hawan sa, zai tabbatar cewa aiki ya zo yi a Jigawa, ba hawa kujera don cika burin siyasa ba. Ƙudirori 12 da Ɗanmoɗi ya yi amfani da su a matsayin ajandar mulkin sa, tun daga farko sun nuna lallai talakawan Jigawa sun yi babban kamu a zaɓen 2023.

Muhimman ayyukan da ya aiwatar a cikin kwanaki 100 na farkon mulkin sa, sun ƙara sa al'ummar Jigawa sakankancewa tabbas direban da ke riƙe da sitiyarin motar su gwararre ne, kuma a kan hanya ya ke ɗoɗar, babu gargada mai fashe taya, kuma motar ba ta tangaɗi.

Kasafin Naira Biliyan 298.14 da Gwamna Namadi ya gabatar a Majalisar Dokokin Jigawa a ranar Talata, batutuwa ne da za su ƙara fito da Jihar Jigawa ta yadda za ta ƙara gogayya da jihohi da dama wajen ci gaba ta fannoni da dama.

Yayin da kasafin wasu jihohin ya nunka na Jigawa kusan sau biyu, amma ayyukan da Gwamna Namadi zai yi wa al'ummar Jihar Jigawa sun yi yawan da mutum zai yi tsammanin ko kasafin ya nunka adadin kuɗaɗen sau biyu shi ma.

Da ya ke mutum ne da ya goge da aiki matuƙa, a jawabin sa wurin gabatar da kasafin, Namadi ya bayyana kafa sabbin hukumomi biyar, ciki har da Hukumar Hana Cin Hanci da Rashawa. Duk gwamnan da ya yi haka a ranar gabatar da kasafin farko na mulkin sa kuwa, tilas ma'aikata da 'yan kwangila su fahimci aiki ya zo, ba da wasa ya ke ba.

Gwamna Namadi ya bijiro da ɗaruruwan ayyukan da suka samar da aikin yi ga ɗimbin matasa, bunƙasa tattalin arzikin jiha, kiwon lafiya, fannin ilmi, raya yankunan karkara da inganta rayuwar al'umma.

Mako ɗaya kafin ya gabatar da kasafin, gwamnatin sa a ƙarƙashin Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Jiha ta fito da shirin ƙara samun kuɗaɗen harajin cikin gida, wanda ake sa ran samun Naira biliyan 42 cikin 2025. Duk gwamnan da ya bijiro da wannan tunani, an san aiki ya zo yi, ba da wasa ya ke ba.

Dama tun daga farkon hawan sa ya fara aikin tantance adadin yawan ma'aikatan Jihar Jigawa baki ɗaya. Kai dai ka san wanda ya fara haka, to ba da wasa ya ke ba.

A ɓangaren ayyukan da Gwamna Namadi ya bijiro da su, za a kashe sama da Naira biliyan 40 wajen gina titina da gadoji a garuruwa da ƙauyuka kimanin 80, ko fiye da haka. Wasu titinan ci gaba da aikin za a yi, wasu kuma kammalawa za a yi, da yawa a cikin su kuma sabbi ne za a fara. Wato Namadi ya nuna muhimmancin raya yankunan karkara sosai a wannan kasafin sa na farko a Jihar Jigawa.

Wasu daga cikin garuruwa da ƙauyukan da za su ci moriyar kwalta a cikin kasafin, akwai: Shuwarin, Wurma, Chamo, Isai, Jigawar Ɗan Ali, Sule Tankarkar, Kwanar Madana, Kaugama, Daƙyayyawa, Warwaɗe, Jahun da Gujungu.

Akwai kuma aikin titina cikin garin Wurma, Kanya Babba, Titin By-pass Gumel, Kafin Hausa, Ɗan sure, Gandun Sarki, Bulangu, Aujara, Basirka, Ɗangyatum da Sankara.

Waɗannan kaɗan ne aka lissafa domin mai karatu ya fahimci irin aikin da Gwamna Namadi ya kinkimo, ta yadda zai tabbatar da cewa aiki ya zo, ba da wasa yake ba. Kuma akwai aikin gadoji da kwalbatoci masu yawa duk a cikin kasafin. Ga kuma aikin shararra, wato 'feeder roads' da za a yi, a ƙarƙashin tallafin Bankin Duniya, a yankuna da dama.

Akwai ayyukan samar da wutar lantarki a yankunan karkara da dama a faɗin jihar, kuma akwai ayyukan kafa fitilun kan titi a garuruwa da ƙauyuka daban-daban.

Gwamnatin Namadi ta fito da Shirin Bunƙasa Ilmi, wato JTEACH, Shirin Inganta Lafiya, wato JHEALTH da kuma Shirin Bunƙasa Harkokin Noma, wato JAGRO.

Idan aka dubi ɓangaren ilimi, za a ga cewa Gwamna Namadi ya yi ƙoƙarin zarce mafi ƙarancin kasafin ilmi na kaso 20% bisa 100% da Hukumar UNESCO ta ƙayyade kowace jiha ta kashe wa fannin ilmi. Domin shi ya ware wa fannin ilmi har kaso 32 bisa 100 na kasafin 2024. 

Yayin da Gwamnatin Namadi za ta kashe Naira biliyan 11.37 a manyan makarantun gaba da sakandare, za ta kashe Naira biliyan 12.15 a makarantun sakandare, sai kuma Naira biliyan 17.37 firamare, UBEC da Shirin Ilmin Tsangaya, wanda aka ƙirƙiro kwanan nan.

Yanzu haka ana nan ana tantance ɗaukar malamai 30,000 domin cike gurbin ƙarancin malamai a makarantun jihar. Duk wanda ya bijiro da wannan aiki a farkon kasafin sa kuwa, kun san aiki ya zo yi, ba da wasa yake ba.

A ƙarƙashin JHEALTH, Kasafin 2024 na Jigawa ya kinkimo aikin ɗaga darajar asibitoci 13 a garuruwa daban-daban zuwa Manyan Asibitoci, wato 'General Hospital', sannan kuma za a gina wasu sabbin Manyan Asibitoci a Ringim, Taura da Kafin Hausa. Mata da ƙananan yara za a riƙa ba su kulawa a ƙananan asibitocin yankuna.

Gwamnatin Namadi ta kinkimo ayyukan raya jiha a fannin noma, a ƙarƙashin shirin JAGRO, inda za a kashe Naira biliyan 36 wajen gudanar da ayyuka da shirye-shirye da dama, waɗanda za su sanar da wadatar abinci da yalwar arziki.

Ɗimbin matasa za su ci moriyar wannan kasafin kuɗi na 2024, idan aka yi la'akari da ayyukan da za su samu a fannonin inganta rayuwar su daban-daban.

Duk a cikin wannan kasafin kuma Gwamna Namadi ya ɗauko aikin gina gidaje a garuruwan Birnin Kudu, Haɗejia, Gumel, Kazaure, Ringim, Kafin Hausa da Baɓura.

Haka nan akwai aikin samar da ruwa a garuruwa da ƙauyuka masu yawan gaske.

Wannan tsakure daga muhimman ayyukan da ke cikin Kasafin 2024 na Gwamna Namadi, ya isa mai karatu ya fahimci tabbas Ɗanmoɗi aiki ya sa a gaba, ba da wasa ya ke ba.


Suleiman Aliyu ya rubuto ne daga Dutse

No comments

Powered by Blogger.