Header Ads

INEC ta nesanta kan ta daga zargin baddala ƙuri'un zaɓen gwamnan Kogi a Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe, IRev

Shugaban INEC

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ko kaɗan ba ta baddala sakamakon zaɓen da ta aika a Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe (IReV) ba.

INEC ta ce ta lura da wasu rahotanni da ta riƙa cin karo da su a kafafen yaɗa labarai, inda ake zargin ta da hargitsa sakamakon zaɓen da ta tura a manhajar IReV, na zaɓen gwamnan Jihar Kogi.

Kogi na ɗaya daga cikin jihohi uku da aka yi zaɓen gwamna, a ranar 11 ga Nuwamba. Sauran jihohin biyu su ne Imo da a Kudu maso Gabas da kuma Bayelsa a Kudu maso Kudu.

Cikin sanarwar da INEC ta fitar a ranar Talata, ta ja yankulan jama'a cewa su yi watsi da zargin hukumar ta baddala sakamakon zaɓen da ta loda a manhajar IReV.

Ta bayyana cewa wannan zargi da aka yi wa hukumar "ƙage ne kawai da ƙarairayin bugar da hankulan jama'a."

Wannan kakkausan martani na INEC na ƙunshe cikin wata sanarwar da Kwamishinan Tarayya na hukumar, Mohammed Haruna ya fitar a ranar Talata.

Haruna ya ce: "Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta lura da wasu rahotanni da ke ɗora mata zargin baddala sakamakon yawan adadin ƙuri'un da ta loda kan Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe, wato IReV, a jihar Kogi. To ko ma daga ina, labarin ya fito dai ƙarya ce.

"Duk mai wata tababa ko shakku ya sani cewa sahihan adadin yawan waɗanda aka tantance karin shaidar zaɓen su na nan killace cikin Na'urar Tantance Adadin Masu Zaɓe (BVAS), wadda da ita ce ake amfani wajen tantance adadin masu rajistar da za su yi zaɓe a ranar zaɓen. Kuma adadin yawan masu zaɓen ha zai taɓa canjawa ba a cikin na'urar."

Haruna ya ce batun duba adadin alƙaluman sakamakon zaɓe a manhaja ya danganta ne idan akwai 'network' ko babu.

Ya ce idan aka tura sakamakon zaɓe a IReV, to ba lallai ne ya isa a lokacin da aka tura ba. Kamar dai yadda saƙon tes na SMS ta waya ya ke, ba lallai ya isa lokacin da aka tura ba. Wani ya kan yi latti.

Daga nan sai ya ƙara da ce aikin Jami'an Zaɓe ne su danna ɗan maɓallin data kan Na'urar Tantance Masu Katin Zaɓe, wato BVAS domin tabbatar da an tura data a manhajar.

INEC ta ce babu inda ta baddala sakamakon zaɓe don a zalinci wani ɗan takara ko a fifita wani ɗan takarar kan wani.

Hukumar ta ce dukkan sakamakon zaɓen da aka gani a jihohin uku, shi ne abin da jama'a suka zaɓa, kuma shi ne INEC ɗin ta bayyana.

Haruna ya yi bayani dalla-dalla cewa babu yadda za a yi a iya baddala sakamakon zaɓen da adadin yawan rajistar da BVAS ta tantance idan an loda shi a manhajar IReV.

Idan ba a manta ba, tun a ranar zaɓe INEC ta fito ƙarara kamar yadda ta saba yi a kowane zaɓe, cewa ba ta da ɗan takarar ko ɗaya. Ɗan takara a cewar ta, na jam'iyya ne da 'yan jam'iyya. Don haka sai wanda jama'a suka zaɓa.

Aikin INEC inji hukumar shi ne shirya zaɓe sahihi kuma karɓaɓɓe, kamar yadda a kowane lokacin ta ke yin bakin ƙoƙarin ta.

No comments

Powered by Blogger.