Header Ads

Gwamnatin Kano za ta kashe sama da Naira biliyan 40 wajen manyan ayyukan raya jiha

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf 

Majalisar Zartaswar Jihar Kano za ta amince a kashe Naira 40,353,117,070 domin aiwatar da wasu manyan ayyukan raya jiha da kuma inganta rayuwa.

Majalisar ta amince da haka ne a taron ta na 8, wanda aka yi a ranar Talata. Na farko dai daga cikin ayyukan sun haɗa da kashe Naira biliyan 15.97 a Ma'aikatar Ayyuka da Gidaje, domin gina Gadar Sama da Titin Ƙarƙashin Ƙasa a daidai Ƙofar Ɗan'Agundi.

Sai kuma Naira biliyan 14.45 da za a kashe wajen wajen gida Gadar Sama a Tal'udu.

Haka kuma majalisar ta amince a kashe Naira biliyan 3.360 wajen gina rufafiyar magudanar ruwa wadda za ta tashi daga Jakara-Kwarin Gogau, sai kuma Naira biliyan 1.579 da za a kashe wajen gina titin baifas daga Ƙofar Waika zuwa Unguwar Daɓai zuwa Yankuje duk a cikin Ƙaramar Hukumar Gwale.

Haka nan a cikin sanar wadda Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Halilu Ɗantiye ya fitar, ya ce an amince a kashe Naira biliyan 1.350 duk dai a Ma'aikatar Ayyuka da Gidaje ɗin, domin gina titin da ya tashi daga Unguwa Uku 'Yan Awaki zuwa Limawa Junction a Ƙaramar Hukumar Tarauni.

Sai kuma aikin Naira miliyan 820 domin ƙarasa aikin titin Kanye-Kabo-Dugabau a cikin Ƙaramar Hukumar Kabo.

Akwai kuma aikin ƙarasa yanka titin Ƙofar Dawakai zuwa Dandinshe zuwa Kwanar Madugu da ake yi zuwa falle biyu, kan kuɗi Naira miliyan 802.

Akwai sauran ayyuka da dama waɗanda majalisar ta amince a fitar domin a yi, duk a wurin zaman na ta na 8.

No comments

Powered by Blogger.