Header Ads

GIDOGA DA GARARUMA: Yadda Matawalle Ya Wawuri Sama Da Naira Biliyan 1 A Harƙallar Gina Otal Da Gidan Shaƙatawa


* An yi watsi da kwangilar bayan an karɓi kashi 93% bisa 100% na kuɗin aiki

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sake fitar da jerin wasu takardu waɗanda suke fallasa yadda tsohon Gwamna, Bello Matawalle ya wawure sama da Naira biliyan ɗaya na aikin ginin otal da muhallin shaƙatawa.
 
Gwamnatin da ta gabata ta Bello Matawalle wanda shi ne Ƙaramin Ministan Tsaro a yanzu, ta kwashe kuɗin da ya kai Naira 1,011,801,545.79 don yin wannan aiki a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
A wata takardar sanarwar manema labarai da Mai magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Laraba, ta ce akwai buƙatar Bello Matawalle ya fito ya yi bayanin kuɗaɗen da ya biya kamfanin '180 Circle Construction and Engineering LTD'.

Sanarwar ta ƙara da cewa, gwamnatin ta Zamfara ta na fito da waɗannan badaƙala ne saboda ya zama izina ga duk wani ma’aikacin gwamnati da ke tunanin zai iya yin yadda ya ga dama da dukiyar al’umma.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Domin tabbatar da gaskiya, nauyi ne da ya rataya a wuyan Gwamnatin Zamfara na ta riƙa bankaɗo waɗannan ayyukan boge da Bello Matawalle ya ƙirƙira a lokacin sa, wanda an samar da su ne don a sace dukiyar jiha, ba don a yi ayyukan ba.

“A ranar 16 ga Yuli, 2020 ne gwamnatin Bello Matawalle ta bayar da kwangilar gina otal da muhallin shaƙatawa ga kamfanin '180 Circle Construction and Engineering LTD'. An ba wannan kamfanin kwangilar ce kan jimillar kuɗi Naira 1,149,288,084.25.
 
“A ranar 7 ga Agusta, 2020, Bello matawalle ya rattaba hannu aka fitar da Naira 344,786,425.27 a matsayin biyan farko ga kamfanin. Sai dai bayan da aka biya wannan kuɗin sai kamfanin ya gudu, ba a sake jin ɗuriyar sa ba sai bayan shekara guda. Wanda wannan ba ƙaramin laifi ba ne a tsarin gudanarwa na gwamnati. 

“Bayan shekara ɗaya da biyan sa waɗancan miliyoyin kuɗi, sai ɗan kwangilar ya dawo. Matakin da gwamnatin Matawalle kawai ta ɗauka shi ne jan kunnen sa, tare da gargaɗin cewa kar ya ƙara aikata hakan. Wannan rashin mutunci da keta ƙa’idar aiki babu inda za a same shi sai a gwamnati wacce mutane irin su Matawalle suke jagoranta.

“Ga hujjoji na yadda aka kwashe ragowar kuɗi da sunan wannan aikin. A ranar 6 ga Yuli 2021, Bello Matawalle ya fitar da Naira 100,420,259.62 zuwa ga kamfanin na 180 Circle Engineering Construction and Engineering LTD. Haka nan a ranar 27 ga Agusta 2021, ya tura Naira 257,060,936.72 ga kamfanin. Har wa yau, a wannan rana ta 27 ga Agusta 2021, Matawalle ya sake tura Naira 185,250,000.00 ga wannan kamfani. 

“Ba iya nan badaƙalar ta tsaya ba, a ranar 24 ga Maris 2022, Ma’aikatar Kuɗi ta Jihar Zamfara ta sake tura Naira 20,000,000.00 ga wannan kamfani na 180 Circle Engineering Construction and Engineering LTD, inda jimillar kuɗaɗen da Matawalle ya kwasa ta hannun kamfanin ya kama Naira 1,011,801,545.79.

“Saboda tsabar rashin imani, duk da saɓa ƙa’idar da aka yi wurin fitar da kaso 93% na kuɗi, maimakon a yi aikin, sai aka watsar. Ƙimar aikin da aka yi a wurin shi ne kaso 29.94% wanda kuɗin sa ya kama Naira miliyan 344,088,384.15. Sama ko ƙasa, an sace Naira miliyan 667,713,161.64.

“Ba zai yiwu mu zura ido ga irin waɗannan manyan ɓarna ba, ko ba komi ya ci karo da tsarin mu na ceto da gina jiha. Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wurin bankaɗowa tare da yin duk mai yiwuwa don ƙwato wa al’umma haƙƙin su. Aikin ceto muka zo yi.”

Wannan ne karo na uku da Gwamnatin Dauda Lawal ta fara bankaɗo badaƙalar da ta ke zargin Matawalle ya aikata a lokacin da ya ke Gwamnan Jihar Zamfara.

No comments

Powered by Blogger.