Header Ads

Allah ya ji kan Shaikh Dk. Yusuf Ali


Marigayi Shaikh Dakta Yusuf Ali

Allah Ya yi wa Sheikh Dk. Yusuf Ali (Sarkin Malamai Gaya kuma limamin Masallacin Sabuwar Gandu) rasuwa jiya Lahadi 05 ga Nuwamba 2023.

Ya rasu yana da shekaru 74 (1949-2023) bayan fama da rashin lafiya, inda ya bar 'ya'ya 38 da jikoki da dama.

Yau Litinin 06/10/2023 za a yi jana'izar marigayin da misalin ƙarfe 1:30 na rana a  Masallacin Murtala, Tudun Maliki da ke Kano.

Jaridar ALMIZAN ba za ta taba mantawa da shi ba saboda irin gudummawar da ya rika ba ta a shekarun baya, sa'ilin da ya shafe shekaru yana buga talla a jaridar. Kuma ya rika tafiyar da wani filin amsoshin tambayoyin masu karatu mai suna ILMI KOGI.

Allah ya ji kansa da gafara.

Hoto: Salilin da marigayin ya ziyarci Shaikh Zakzaky a gidansa a shekarun baya. Sun yi makarantar SAS Kano tare 

No comments

Powered by Blogger.