Header Ads

Saboda maulidi, Gwamnatin Iran ta yi wa fursunoni dubu afuwa

Jogoran juyin-juya-halin Musulunci na Iran 
Gwamnatin jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi afuwa ga sama da fursunoni 1,000 daga gidajen yarin ƙasar domin murnar bikin Maulidin Annabi Muhammad (SAW).

Wata kafar yaɗa labarun gwamnati ta ce an kuma sassauta hukuncin kisa da aka yanke wa mutane 54.

Dama dai jagoran juyin-juya-halin Musulunci na ƙasar, Ayatollah Ali Khamenie kan yi afuwa ga fursunoni a lokutan murna na addinin Musulunci.

No comments

Powered by Blogger.