Header Ads

Mun yi sabon tsarin yaƙi da ta'addanci da rashin tsaro - Tinubu

Daga BOLA AHMED TINUBU

JAWABIN MAI GIRMA, SHUGABA BOLA AHMED TINUBU, GCFR, SHUGABAN ƘASA KUMA BABBAN KWAMANDAN ASKARAWAN NIJERIYA A CIKAR JAMHURIYAR TARAYYAR NIJERIYA SHEKARU 63 DA SAMUN ‘YANCIN KAI, RANAR LAHADI 1 GA OKTOBA, 2023

‘Yan'uwa na ‘yan Nijeriya,
 
Ina farin cikin yi maku jawabi a yau, ranar cikar ƙasar mu shekaru 63 da samun ‘yancin kai, a matsayi na na shugaban ƙasar mu mai albarka, kuma zallar ɗan'uwan ku ɗan Nijeriya.

2. A wannan rana mai muhimmanci mai cike da fatan alheri, mu na jinjina ga iyayen mu da su ka kafa Nijeriya, mazan su da matan su. Ba don su ba, da ba a samu ƙasar Nijeriya ba. Gwagwarmayar su, sadaukarwar su da jagorancin su ne su ka haifar da 'yantacciyar ƙasar Nijeriya mai mulkin kan ta.

3. A wannan lokacin, mu na ƙarfafa wa juna gwiwar cewa a matsayin mu na ‘yan Nijeriya, Allah ya yi mana baiwa a dunƙule da kuma a ɗaiɗaikun mu. Babu wanda ya fi wani a cikin mu. Nasarorin da Nijeriya ta cimma su ne abin alfaharin mu. Ƙalubalen da mu ka jure wa su ne ke ƙarfafar mu. Kuma babu wata ƙasa ko wani iko a duniya da zai iya dankwafe mu daga isa matsayin da ya dace da mu. Wannan ƙasar taku ce, ‘yan'uwa na. Ku so ta, ku karrama ta a matsayin ta na ƙasar ku ta kan ku.

4. Nijeriya ta isa ƙasa a bar misali bisa yanayin zubi da tsarin ta. Allah ya azurta mu da ƙabilu, addinai da al’adu daban-daban. Sai dai danƙon zumuncin da ke tsakanin mu ya na da matuƙar ƙarfi ko da yake ba ganin sa ake ba. Mun haɗu kan buri guda ɗaya na samar da zaman lafiya da cigaban al’umma, da fata guda ta bunƙasar arziki da haɗin kai, da kuma manufofin haɗaka na juriya da adalci.

5. Samar da ƙasa da aka ɗora bisa harsashin aiwatar da waɗannan manufofi masu daraja kan al’ummomi mabambanta ya zamo aiki mai matuƙar albarka da yake fama da ƙalubale. Waɗansu mutanen sun ce bai kamata a samu ‘yantacciyar ƙasar Nijeriya ba. Wasu sun ce ƙasar mu za ta rushe. Har abada su na bisa kuskure. A nan, ƙasar mu ta kafu kuma a nan za ta tabbata.

6. A bana, mun tsallake wani siraɗi mai muhimmanci a tafarkin mu na tabbatar da cigaban Nijeriya. Zaɓen da mu ka yi wa gwamnatin dimokiraɗiyya ta bakwai a jere na nuna cewa ƙasar mu ta yi riƙo da tsarin dimokiraɗiyya da aiki da doka.

7. Ranar da na kama mulki, na ɗauki alƙawurra kan yadda zan shugabanci wannan babbar ƙasa tamu. Daga cikin alƙawurran har da yi wa tattalin arzikin mu garambawul domin samar da tsaro ga rayuka, ‘yanci, da walwalar al’umma.

8. Na ce ɗaukar tsauraran matakai ya zama wajibi domin ɗora ƙasar mu kan tafarkin walwala da bunƙasar tattalin arziki. A ranar na sanar da kawo ƙarshen tallafin man fetur.

9. Ina sane da wahalhalun da su ka biyo baya. Idanu na su na gani kuma zuciya ta ta na ƙunci. Ina son in bayyana maku dalilin da ya sa wajibi mu ci gaba da daurewa a cikin wannan mawuyacin hali. Waɗanda ke son a ci gaba da tallafin man fetur da mummunan tsarin sauyin kuɗaɗen waje mutane ne da ke son gina tafka-tafkan gidaje a cikin fadama. Ni ba haka na ke ba. Ni ba zan gina mana gida a bisa tubalin toka ba. Idan mu na son gidan mu ya yi ƙwari, ya daɗe, dole ne mu gina shi kan tsandauri.

10. Gyara abu ne mai ciwo, amma shi ne abin da cigaban mu da ɗaukakar mu ke buƙata. A yanzu mu na ɗauke da wahalhalun da za su kai mu zuwa ga makomar da za a raba arzikin ƙasar mu mai yalwa bisa adalci ga kowa da kowa maimakon wasu tsirarun mahandama su tattare a wurin su. Za mu samar da Nijeriyar da za a mayar da yunwa, fatara da wahala su zama tsohon labari.

11. Ba na farin cikin ganin al’ummar ƙasar nan na fama da wahalar da ya kamata a ce an sauke ta a shekarun da su ka wuce. Zan so a ce babu waɗannan wahalhalun a yanzu. Amma dole ne mu daure idan mu na son samun makoma tagari.

12. Gwamnati na na yin bakin ƙoƙarin ta wurin sassauta wannan wahala. Yanzu zan bayyana maku matakan da mu ke ɗauka domin rage wannan raɗaɗin da magidanta da iyalai ke fama da su.

13. Mun fara ɗaukar matakan sauya tsarin tafiyar da gwamnati domin samar da daidaton tattalin arziki, yaƙi da hauhawar farashi, bunƙasa ayyukan masana’antu, samar da tsaron rayuka da dukiya da kuma tallafa wa talakawa da sauran mabuƙata.

14. Bisa tattaunawar mu da ƙungiyar ƙwadago, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, mu na gabatar da ƙarin albashi na farko inda za mu ƙara mafi ƙarancin albashin Gwamnatin Tarayya ba tare da ƙara hauhawar farashi ba. A tsawon watanni shida masu zuwa, ƙananan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya za su samu ƙarin naira dubu ashirin da biyar kowanne wata a albashin su.   

15. Domin kawo cigaba a yankunan karkara, mun kafa asusun tallafi kan samar da kayayyakin more rayuwa domin jihohi su bunƙasa ɓangarorin da ke da muhimmanci a yankunan su. Tuni jihohi su ka karɓi kuɗi domin ba da tallafin sassauta raɗaɗin hauhawar farashin abinci da sauran buƙatun yau da gobe.

16. Bunƙasa tattalin arziki ta hanyar rage farashin sufuri na da matuƙar muhimmanci. Dangane da haka ne mu ka buɗe wani sabon babi a fannin sufuri ta hanyar samar da motocin haya masu amfani da iskar gas a faɗin ƙasar nan. Waɗannan motoci za su caji kuɗi mai sauƙi da bai kama ƙafar yadda ake biya yanzu ba.

17. Ba da jimawa ba kayan aikin sauya motoci masu amfani da fetur zuwa gas za su fara isowa ƙasar nan saboda mun ɗauki matakan taƙaita lokacin da aka saba ɗauka kafin shigo da su. Kuma za mu kafa wurin ba da horo a faɗin ƙasa domin koyarwa da ba da sababbin damarmaki ga masu harkar sufuri da kuma masu kafa masana’antu. Wannan lokaci ne mai muhimmanci da ƙasar mu ta rungumi hanya mafi inganci wurin samar wa tattalin arzikin mu makamashi. Samar da wannan sauyin, kafa sabon tarihi ne.

18. Na ɗauki alƙawarin tsaftace ɓarnar da ta yi wa Babban Bankin Nijeriya dabaibayi. Wannan aikin an riga an fara shi. An kafa sabon shugabanci a Babban Bankin. Kuma mai bincike na musamman da na naɗa na gab da gabatar da rahoton sa kan kurakuran da aka samu a baya da kuma hanyoyin da za a magance aukuwar hakan nan gaba. Daga yanzu, dokokin mu na tasarrufi da kuɗi za su amfani kowa da kowa ne maimakon masu iko da masu kuɗi kaɗai.

19. Dokar haraji mai hikima na da muhimmanci ga cigaban tattalin arziki da adalci. Na ƙaddamar da kwamitin sauya fasalin tsarin haraji domin inganta tattara haraji a ƙasar nan da kuma magance dokoki marasa adalci ko masu kawo tarnaƙi ga cigaban kasuwanci da bunƙasar tattalin arziki.

20. Domin bunƙasa samar da aikin yi da kuɗin shiga ga mazauna birane, mun samar da asusun zuba jari ga kamfanonin da su ka nuna alamar makoma tagari. Haka kuma mun ƙara zuba jari a ƙanana da matsakaitan kamfanoni.

21. Daga wannan watan, za a ƙara gidaje miliyan 15 kan waɗanda ake bai wa tallafin kuɗi kai-tsaye domin rage masu raɗaɗi.

22. Gwamnati na a ko da yaushe za ta ci gaba da bai wa tsaron al’umma muhimmancin gaske. Mun bunƙasa hanyar haɗin kai da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro. An ɗora wa manyan hafsoshin soji muhimmin aikin farfaɗo da karsashin rundunoni mu.

23. A nan, ina jinjina da yabo ga dakarun tsaron mu da su ke ba mu kariya tare da tabbatar da tsaron ƙasar mu. Da yawan su sun riga mu gidan gaskiya. Mu na tuna su a yau tare da iyalan su. Za mu bai wa dakarun mu kayan aikin da za su sauke nauyin da ke kan su a madadin al’ummar mu.

24. Za mu ci gaba da naɗa mutane bisa muhimman muƙamai daidai da tanadin tsarin mulki na yin adalci ga kowa. Za a ci gaba da kulawa da mata, matasa da masu buƙatu na musamman a waɗannan naɗe-naɗen.

25. Zan yi amfani da wannan dama domin taya Majalisun Dokoki na Ƙasa murna kan rawar da su ka taka wurin kafuwar wannan gwamnati ba tare da ɓata lokaci ba ta hanyar gudanar da ayyukan da tsarin mulki ya ɗora masu na tantance waɗanda za a naɗa da kuma sa ido kan yadda su ke gudanar da ayyukan su.

26. Haka kuma ina taya ɓangaren Shari’a murna a matsayin su na ginshiƙin dimokiraɗiyya da adalci.

27. Ina kuma taya murna ga ƙungiyoyin mu na cigaban al’umma da ƙungiyoyin ƙwadago bisa sadaukarwar su ga dimokuraɗiyyar Nijeriya. Ba ko da yaushe ra’ayin mu kan zama ɗaya ba amma ina mutunta shawarwarin ku. Ku ‘yan'uwa na ne kuma ina girmama ku.

28. ‘Yan'uwa na ‘yan Nijeriya, tsoro ko ƙiyayya ba za su kawo mana cigaba ba. Za mu iya samun ingatacciyar Nijeriya ne kaɗai ta hanyar ƙwarin gwiwa, tausayi da kuma sadaukar da kai a matsayin dunƙulalliyar ƙasa guda.

29. Na yi alƙawari zan ci gaba da mayar da hankali tare da bauta maku cikin amana. Ina kuma gayyatar kowa ya ba da gudunmawa wurin cigaban ƙasar mu abar ƙaunar mu. Za mu iya. Ba makawa za mu yi. Kuma tabbas za mu yi nasara!

30. Baki ɗayan ku ina taya ku murnar cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai.

31. Na gode da sauraro.

32. Allah ya albarkaci Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya.

No comments

Powered by Blogger.