Header Ads

Matasan Arewa maso Gabas Sun Ƙalubalanci Gwamnonin Arewa Su Yi Koyi Da Ayyukan Gwamnan Kano

Matasa a ƙarƙashin Ƙungiyar 'North East Youth Progressive Union' and Coalition for Democratic Rights Group', sun ƙalubalanci Gwamnonin Arewa su yi koyi da irin ayyukan inganta rayuwar al'umma, wanda Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ke aiwatarwa.

Matasan sun yi wannan kira a ranar Laraba, a Yola, babban birnin Jihar Adanawa, inda suka yi taron manema labarai.

Idan za a tuna, Gwamnatin Jihar Kano a ƙarƙashin Gwamna Yusuf ta sake farfaɗo da inganta ilmin 'ya'yan talakawa, wanda tsohon Gwamna Sanata Rabi'u Kwankwaso ya ƙirƙiro a zamanin mulkin sa.

Shiri ne wanda ke bai wa 'ya'yan talakawa damammakin samun guraben tafiya karatu kyauta a jami'o'in ƙasar nan da na ƙasashen waje.

Kwanan nan Gwamnatin Kano ta ɗauki nauyin ɗalibai 1001 waɗanda suka tafi ƙaro karatu a Indiya da Uganda kyauta.

Da ya ke jawabi wurin taron manema labarai, Shugaban Ƙungiyar Dakta Kabir Hassan Sambo, ya nuna damuwar sa dangane da bambancin ratar samun damar ilmi tsakanin Arewa da Kudancin ƙasar nan.

Sambo ya daga nan sai ya bayar da shawarar cewa gwamnonin Arewa su gaggauta ɗaukar salo da tsarin da Gwamnatin Kano ke kai na inganta fannin ilmi, a wannan yanayi da ake fuskantar ƙalubalen rayuwar zamantakewa da ta tattalin arziki.

Sambo ya ce: "Abin dubawa ne sosai ganin yadda Gwamna Yusuf na Jihar Kano a cikin watanni biyar ya biya kuɗaɗen ɗalibai, kuɗin abincin 'yan makaranta, kuɗin hayar ɗakunan kwanan dalibai 1001 da aka ɗauka suka tafi karatu Indiya.

"Kuma ya biya kuɗin jarabawar NECO ga ɗaliban sakandare 57,000. Sai kuma kuɗin makaranta ga ɗalibai 7,000 a Jami'ar Bayero da wasu manyan makarantu a Kano, waɗanda aka rage wa kashi 50% bisa 100% na kuɗin makarantun jami'o'i.

"Sannan kuma ya samar da cibiyoyin koyon sana'o'i ga matasa har guda 26 a faɗin jihar, domin tallafa masu a Jihar Kano.

"Gaskiya mu na buƙatar dukkan gwamnonin Arewa su yi koyi da tsare-tsaren da Kano ta ke kan yi, wajen bayar da fifiko kan ilmi da bunƙasa rayuwar al'umma."

Da ya ke bayyana muhimmancin tasirin siyasar Kano da na tattalin arzikin ta a Arewa, Sambo cewa ya yi, "mu na sane da irin yadda Kotun Ƙararrakin Zaɓe ta soke zaɓen wannan jajirtaccen gwamna mai ƙoƙarin farfaɗo da tasirin matasan Arewacin Najeriya. To kamar sauran matasan Kano, mu ma mun zuba ido domin ganin yadda za ta kasance a Kotun Ɗaukaka Ƙara. Don haka tilas a yi adalci. Saboda adalci shi ne ginshiƙin ɗorewar dimokraɗiyya."

Ya kuma yi kira da godiya dangane da irin yadda Gwamnatin Kano ta karɓi ɗimbin masu gudun hijira daga Arewa maso Gabas, a lokacin yaƙin Boko.

Ya tuna da yadda Gwamnatin Kano ta riƙa bayar da horo ga matan da suka rasa mazajen su da zawarawa, ana koyar da su sana'o'in hannu daban-daban. Sannan kuma aka riƙa shigar da marayu makarantu daban-daban a Kano.

No comments

Powered by Blogger.