Header Ads

JAWABIN JAGORA SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) DANGANE DA ‘PASSPORT’ DIN SU DA AKA BA SU

Da yake ganawa da ba’adin ‘yan uwa Musulmi a ranar Mauludin Manzon Allah (S) -17 ga Rabi’ul Auwal 1445 (2/10/2023)- a gidansa da ke Abuja, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ambata cewa:

“Kuma na so in muku wani albishir da cewa, ainihin ‘Passport’ din nan da aka yi ta fafutukar a samu, to dai yanzu yana hannu. A karshe, su da kansu suka zo nan har gida suka dauki hotuna da duk abubuwan da ake bukata wanda akan yi a ofis din, sun zo har gida suka yi mana, kuma suka aiko da Fasfo din, insha Allah.

“Saboda haka yanzu muna ‘yan shirye-shirye ne na kama hanya, mun shirya da asibitocin da za mu je, da kuma likitocin da za su yi aikace-aikace, saboda haka ba da jimawa ba, insha Allahu za a dan ji mun dan fita. Insha Allah.

“To, muna godiya Allah Ta’ala, da kuma sadaukarwar ‘yan uwa da yawan gaske. Na ji wadansu har suna surutai, wani yana cewa, wai ‘yan Shi’a a kan Passport takardar banza wai su sun yi shahada. Nace, ba kan passport suka yi Shahada ba, ‘Fisabilillahi’ suka yi. Su wadanda suka ga taron, haushin da suke ji shi ne, duk wani abu da yake bayyana izzar addinin nan tsoro yake basu. Koma wane iri ne. Shi yasa kaga suke adawa da duk wani abu. Suna son kowa ya yi shiru ne.

“Mauludin nan suna son kowa ya yi zamansa a gida ne, yace yana son Annabi (S) a zuciyarsa. Da zaran an fito, to ya nuna izzar addini, kuma haushi suke ji. To duk wani lokaci da suka ga kuma abin da ya shafi Harkar nan, in dai suka ganshi a bayyane, haushi suke ji. Shi yasa su kuma ‘yan uwa ko da wane lokaci akan samu wani dalili da zai sa ko da wane lokaci a rika nuna izza din, don fitowar namu izzar ce. 

“Idi ainihin an yi shi ne don nuna izza shi ma, don haka aka koyar da mu cewa, a taru ne a tsakiyar gari, a fita ta hanya guda ana Azkar, in an gama Idin a dawo ta wata hanya tadaban, ba wadda aka fita zuwa Idin ba, sannan a sake haduwa a tsakiyar garin inda aka fara, sannan kowa ya kama hanyar gida. To, da za a yi haka nan a gari guda, ace a hadu duk guri daya, kuma a dawo ta wata hanya daban. Haba! Ai ka ga zai nuna izzar wannan al’ummar.

“To, haka nan duk abin da suka ga muke yi, wanda yake nuna martaban iyalan gidan Annabi (S) haushi yake basu ai. Mauludi yana nuna son Annabi (S) ne, sauran ‘Marasim’ na A’imma (AS) yana nuna ana raya abin da ya shafi iyalan gidan Annabi (S) din ne, don haka kowanne yana basu haushi. Suna jin haushin Ashura, suna jin haushi Mawalid da muke yi na A’imma (AS), duk wani taro namu, kai ko mene ne namu ma.

“Saboda haka, babu wani wanda ya yi shahada kan wani abu ‘in particular’. Alal misali, wanda aka kashe ranar Quds, ba za ka ce musu sun yi Shahadar Quds ba, Fisabilillahi suka yi. Wanda aka kashe ranar Ashura, ba sunansa Shahadar Ashura ba, sunansa Shahada Fisabilillahi. Wanda aka kashe ko ma a kan mene ne, in dai an kashe shi a kan ‘manifestation’ na addini ne, to saboda addini ne. Shi ma cewa, lallai a sakar mana fasfuna dinmu, ya nuna cewa an samu wadansu mutane da su ba su yarda a zalunce su ba. Suna neman hakkinsu ta kowane hali. Kuma abin da basu so kenan, suna son a yi musu shiru ne kar a ce komai. Yauwa.”

Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “wannan alama ce da ke nuna mutane (da suka rika Muzaharori) sun yi ne saboda nuna izzar addini, kuma haqa ta cimma ruwa insha Allahul Azeem.”

Sannan ya kuma mika godiyarsa ga Allah (T) da cewa: “Kuma mun godewa Allah Ta’ala, duk da mun zauna da rashin lafiyar da ga yadda aka saba bisa dabi’a Dan Adam ba zai yiwu ya rayu da irin wannan rashin lafiyar ba, amma kuma da yake Allah ne mai rayawa, sai ya raya mu haka nan din.”

Yace: “Amma duk da haka dai da lalurori, musamman kuna iya ganin Malama yadda take takarkarowa babu kafa, tun 2016, yau shekara bakwai cur tana sallah a kujera ne, to amma kuma haka nan, yana dada tabarbarewa ne al’amarin guiwan nata, ba don kiyayewar Allah ba.”

Yace: “Mun yi sa’a, lokacin da aka kai mu ‘prison’ na yi ta jin tsoron kar abin ya taso mata, don takan yi kamar ba za ta yi rai ba (idan ya tashin), to sai kuma dai bai taso ba sam har izuwa ma fitowar mu din nan, bai sake tasowa ba, amma ya rika tasowa (lokacin) muna tsare a hannun DSS. Har ma a Kaduna (lokacin ana wajen DSS) ya taso ya yi tsanani sosai. To dai kiyayen Allah ne kawai, mun godewa Allah bisa kiyayewar da ya mana da abin da yake bisa ka’idar dabi’a ba za a rayu da shi ba, kuma dai da yake Allah ne mai rayawa, shi ya raya mu din.”
Rubutawa: Saifullahi M. Kabir
03/10/2023

No comments

Powered by Blogger.