Header Ads

Gwamnatin Tinubu za ta ba da fifiko wajen amfani da na'urorin zamani a gidajen rediyo da talbijin - Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa amfani da kayan aiki na zamani a gidajen rediyo da talbijin na da muhimmanci ga gwamnatin Bola Tinubu.

Haka kuma ya jaddada alwashin gwamnati na bai wa harkokin bunƙasa kayan aikin rediyo, talbijin da shirya finafinai goyon baya saboda muhimmancin su ga bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce su na a sahun gaba wajen samun nasarar inganta tattalin arziki a ƙarƙashin ajandar Farfaɗo da Martabar Nijeriya ta 'Hope Agenda' da gwamnatin Tinubu ta himmatu a kai.

Da ya ke jawabi wurin taron AFRICAST na 13 a ranar Talata, otal ɗin Marriot da ke Ikeja, Legas, ministan ya nuna farin cikin sa, ganin yadda taron ya kasance ƙasaitacce, duba da yadda ya ke tafiya bisa kyakkyawan shugabanci, ake bajekolin ilmi da kuma samun damarmakin bunƙasa kasuwancin fasaha da na'urorin zamani.

Ya ce Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NBC) ta ƙirƙiro AFRICAST ne ganin yadda ake samun yawaitar kafa gidajen rediyo, talbijin da bunƙasar harkokin finafinai da sauran kafafen isar da saƙo.

Idris ya yaba wa masu shirya taron, wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar NIFS, ya ce taron ya samar da wani dandalin da ƙwararru a harkokin finafinai da talbijin za su samu dama da lasisin bayyana hajar su.

Ya bayyana muhimmancin rawar da masu ƙirƙiro shirye-shirye, furodusoshi da masu yaɗa shirye-shirye ke takawa wajen nishaɗantarwa a duniya.

Sai ya nuna muhimmancin a riƙa samar da shirye-shirye masu nagarta wajen nishaɗantarwa da ilmantarwa.

Ministan ya jaddada ƙoƙarin da gwamnati ke yi domin komawa amfani da tsarin DSO wajen yaɗa labarai, tare da himma wajen rungumar duk wata hanyar yaɗa labarai ta zamani da ake amfani da ita a duniya.

Ministan, wanda ya riƙa bi ya na duba kayayyakin na'urorin yaɗa labarai da watsa shirye-shirye na zamani waɗanda aka bajekolin su a wurin, ya yaba da irin cigaban da aka samu ta hanyar ƙirƙiro sababbin na'urorin sauƙaƙa ayyukan yaɗa labarai da shirye-shirye.

Ya ce Shugaba Tinubu zai kasance jagora wajen rungumar shirin amfani da na'urorin zamani a kafafen yaɗa labarai a gidajen rediyo da talbijin na Gwamnatin Tarayya.

No comments

Powered by Blogger.