Header Ads

Gwamnan Neja ya taya Ndace murna kan naɗin sa a matsayin shugaban Muryar Nijeriya

Jibrin Baba Ndace

Gwamna Mohammed Bago na Jihar Neja ya miƙa saƙon taya murna ga Alhaji Jibrin Baba Ndace saboda naɗa shi Darakta-Janar na gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi.

Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Malam Bologi Ibrahim, ya raba a ranar Juma'a a Minna.

Gwamnan ya bayyana naɗin a matsayin abin da ya dace, sannan ya ce Baba-Ndace ƙwararren ɗan jarida ne wanda ya yi tasiri a harkar yaɗa labarai.

Ya ƙara da cewa ba ya da shakka ko kaɗan cewa sabon darakta-janar ɗin ya na da ƙwarewa da ƙarfin da zai haɓaka hukumar rediyon ta VON.

Yayin da ya ke bayyana shauƙin cewa sabon shugaban na VON zai zama abin alfahari ga musamman Jihar Neja da ma Nijeriya ita kan ta, sai ya yi alƙawarin zai ba shi dukkan goyon bayan da domin ya cimma nasara a aikin da aka ɗora masa.

No comments

Powered by Blogger.