Header Ads

Bayan Nasara A Kotun Ƙoli, Shugaba Tinubu Zai Ci Gaba Da Aikin Gina Nagartacciyar Ƙasa - Idris

Alhaji Mohammed Idris

JAWABIN MINISTAN YAƊA LABARAI DA WAYAR DA KAI, ALHAJI MOHAMMED IDRIS, A TARON MANEMA LABARAI, DANGANE DA HUKUNCIN SHARI'AR ZABEN SHUGABAN ƘASA DA KOTUN ƘOLI TA YANKE 

Bayan sallama.

1. Bari in fara da yi maku barka da zuwa wannan taron manema labarai, wanda mu ka shirya bayan hukuncin shari'ar da Kotun Ƙoli ta yanke jiya. Hakan ya kawo ƙarshen ƙorafe-ƙorafen ƙararrakin da aka riƙa shigarwa a kotuna game da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

2. Kotuna dai sun zartas da hukuncin su, shi kuma Shugaban Ƙasa da APC sun yi maraba-lale da wannan nasara da kotunan su ka tabbatar.

3. Mun gode wa kotuna saboda juriyar gudanar da wannan gagarumin aiki, wanda su ka nuna haƙiƙanin sauke nauyin da dokar ƙasa ta ɗora masu, a matsayin su na wurin kai kuka ko ƙorafin da ya shafi zaɓe na ƙarshe a matakan shirya zaɓe a ƙasar nan.

4. Yanzu dai mun wuce maganar shari'ar zaɓen Shugaban Ƙasa, yanzu lokaci ne da za mu tunkari aikin tafiyar da gwamnati ba tare da wani abu ya ɗaukar mana hankali ba.

5. Tabbas wannan babban ƙalubale ne, musamman a wannan lokaci da tattalin arziki ke fuskantar mawuyacin hali, ba a Nijeriya kaɗai ba, har duniya baki ɗaya.

Saboda haka tilas mu taru mu haɗa hannu wuri ɗaya, domin magance wannan ƙalubale da ke tunkarar mu. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a fili cewa shi Shugaban Ƙasa ne na kowane ɗan Nijeriya, ba tare da bambancin yanki, ƙabila, siyasa ko addini ba.

6. Tun bayan hawan sa mulki a ranar 29 ga Mayu, ya na ta aiki tuƙuru wajen ƙoƙarin samun nasarar Ajandar Farfaɗo da Nijeriya, wadda ta na daga cikin dalilan sa na kishin zama shugaban ƙasa.

Ya aiwatar da manyan tsare-tsaren da duk da yake dai su na da tsauri sosai, to amma tsaurin na wani taƙaitaccen lokaci ne. Kuma ta haka ne aka gina tubalin girka ƙasaitaccen tattalin arziki, samar da yalwar da kowane ɗan Nijeriya ya cancanci ya samu.

7. Kamar yadda ku ka sani, cire tallafin fetur abu ne ya samo tushe daga Dokar Fetur ta 2021, wadda yanzu ta ke ƙara tanadar wa Gwamnatin Tarayya da Jihohi maƙudan kuɗaɗen da za su riƙa yin ayyukan inganta rayuwa da bunƙasa ƙasa.

8. Sabon tsarin hada-hadar musayar kuɗaɗen waje, an bijiro da shi ne domin toshe ramukan da kuɗaɗe ke zurarewa tsawon shekaru da dama. Hakan kuwa ya na janyo wa gwamnati asarar biliyoyin dala.

9. Waɗannan tsauraran tsare-tsaren sun taru sun yi wa 'yan Nijeriya rubdugun dukan da su ke jin jikin raɗaɗin tsadar rayuwa, lamarin da Shugaban Ƙasa bai taɓa kauda kai ko yin biris da shi ba.

10. Babu gwamnatin da ta san abin da ta ke yi za ta jefa al'ummar ta cikin halin ƙunci da gangan. Shi ya sa mu ke jaddada cewa wannan hali da ake ciki zai wuce cikin taƙaitaccen lokaci nan gaba. Daga nan sai mu shiga yanayin yalwa da sawaba.

11. A ranar 1 ha Oktoba, 2023, Shugaba Tinubu ya ce, "Tsare-tsaren da aka bijiro da su akwai ƙuntatawa, amma fa sai an sha wuya akan sha daɗi. Ba abin farin ciki ba ne mu riƙa ganin 'yan Nijeriya na ci gaba da fama da tsadar rayuwar da tuni ya kamata a ce mun wuce wurin. Na yi fatan cewa da ma ba mu tsinci kan mu cikin wannan mawuyacin hali ba. Amma kuma tilas mu ci gaba da juriya domin kafin a sha zuma sai an sha hayaƙi. Gwamnati na ta na bakin ƙoƙarin ta domin sauƙaƙa wa 'yan Nijeriya tsadar rayuwar da su ke fama da ita."

12. Gwamnatin Tinubu na ɗaukar dukkan matakan da su ka wajaba domin sauƙaƙe wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwar da su ke fama da ita a yanzu. Daga cikin hanyoyin akwai:

a. Ƙarin Naira 35,000 kan albashin ma'aikata, har tsawon watanni shida a jere.

b. Kafa Asusun Gina Ayyukan Raya Ƙasa na Jihohi.

c. Ƙaddamar da sayen motoci na masu aiki da gas, domin sauƙaƙa tsadar zirga-zirgar motoci.

d. Sa hannu kan Dokar Ƙarfin Ikon Shugaban Ƙasa har guda biyar, domin inganta harkokin kasuwanci da ƙara wadata kuɗaɗen hada-hadar musayar kuɗaɗen waje.

e. Kafa Kwamitocin Tsarin Kuɗaɗe da Kwamitin Sauya Tsarin Karɓar Haraji. Kuma an rage wa 'yan Nijeriya yawan haraji.

f. Mu na kusa ga kammala shirye-shiryen fara biyan tallafin Naira 25,000 ga mutum miliyan 15, kuɗaɗen da za a tsittsinka masu a cikin watanni uku.

g. Shugaban Ƙasa ya bayar da umarnin a fitar da metrik tan 200,000 na kayan abinci ga marasa galihu a jihohi 36 da Gundumar Babban Birnin Tarayya domin hakan ya rage tsadar farashin kayan abinci. Sai kuma metrik tan na takin zamani, iri da sauran kayan aikin gona ga manoma.

h. Shirin bayar da lamuni ga ƙanana da matsakaitan masu sana'o'i, wanda Shugaban Ƙasa zai ƙaddamar ba da daɗewa ba. Za a raba naira biliyan hamsin lamuni ga masu sana'o'i miliyan 1 daga yanzu zuwa Maris, 2024. Sai kuma naira biliyan 75 da za a bai wa masu masana'antu da sauran su.

i. Mun ƙaddamar da shirin 3MTT domin horas da dabarun fasaha ga matasa miliyan 3 daga nan zuwa 2025.

j. Shirin NATEP wanda aka ƙaddamar, domin samar wa matasa miliyan 1 ayyuka nan da shekaru 5.

k. Nan da 2024 za mu fara shirin bai wa ɗalibai rance. 

13. Wasu daga cikin waɗannan shirye-shirye ana kan aiwatar da su, ko kuma za a gudanar da su tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi.

14. Waɗannan fa daban ne, domin su ma jihohi su na ta bijiro da nasu tsare-tsaren daban-daban, domin amfanar jama'a.

15. Ba za mu taɓa sauka daga kan turbar nauyin da ke kan mu a matsayin Gwamnatin Tarayya ba, amma ya na da muhimmanci mu bayyana cewa ba za mu iya cimma waɗannan nasarori mu kaɗai ba. Jihohi da ƙananan hukumomi su ma su na da gagarumar rawar da za su taka.

16. A wannan makon yayin Taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya (FEC), a ranar Litinin, an amince da wasu kuɗaɗen da za a bai wa jihohi domin su kai ga nasarar wasu tsare-tsare, ciki har da samun damar cimma nasarar ilmantar da 'yan mata.

17. Ana kan aikin tsare-tsaren Kasafin Kuɗi na 2024. Saboda haka 'yan Nijeriya su kwantar da hankalin su. Wannan kasafin kuɗin na farko na Gwamnatin Tinubu zai kasance na farko wanda kacokam ya maida hankali kan samar da bunƙasar tattalin arziki da samun yalwa ga kowa da kowa.

18. Ina ƙara yin kira ga 'yan Nijeriya da mu ci gaba da haƙuri, ƙasar nan za ta warware, ta bunƙasa ba da daɗewa ba.

19. Mu na fatan samun ƙasaitacciyar ƙasar da kowa zai amfana da cin moriyar bunƙasar ta.

20. A namu ɓangaren, za mu ci gaba da gudanar da aiki tsakani da Allah, yadda al'umma ba za su riƙa tababa ko shakkun gaskiya da sahihancin bayanan da mu ke yaɗa maku na aikace-aikacen gwamnati ba.

21. Zan rufe jawabi nawa da wani kalami da Shugaba Bola Tinubu ya yi, bayan bayyana hukuncin Kotun Ƙoli, inda ya ce: "Ajandar Farfaɗo da Nijeriya zuwa ƙasaitacciyar ƙasa ta ƙara samun karsashi. Zan ci gaba da yin aiki ba dare ba rana domin gina ƙasar da ta cancanci nagartattun mutane irin ɗaukacin mu baki ɗaya ke fatan samu."

22. A nan, ni ma ina ƙara gode maku da samun damar halartar wannan taron manema labarai.

Alhaji Mohammed Idris, fnipr
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai
Abuja, Nijeriya
27 ga Oktoba, 2023

No comments

Powered by Blogger.