Header Ads

Ba mu yarda a yi amfani da zaɓen Gwamnan Kano don a karya tasirin dimokraɗiyya a Arewa ba - CDR Bauchi

Gamayyar Ƙungiyoyin Kare 'Yancin Dimokraɗiyya (CDR) a Jihar Bauchi, sun nuna rashin amincewa da kuma yin tsokaci kan yadda Kotun Shari'ar Zaɓen Gwamnan Kano ta yanke hukuncin da ya haifar da shakku da zargin yunƙurin danne haƙƙin zaɓen da ɗimbin jama'a su ka yi, bisa kyakkyawan tsarin dimokraɗiyya.

CDR ta hasala ne dangane da hukuncin da kotun a Kano ta yanke, wanda ta ce jam'iyyar mai mulki a ƙasa, APC ce ɗan takarar ta na zaɓen gwamna a Kano su ka yi nasara, ba Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP da jama'a su ka zaɓa, kuma INEC ta tabbatar ba.

"Akwai matuƙar buƙatar mu tunatar wa majiɓinta wannan al'amari da dukkan masu ruwa da tsaki cewa, Kano ita ce cibiya kuma ginshiƙin tattalin arzikin Najeriya. "Don haka ƙoƙarin bijirowa ko cimma hargitsi na siyasa yanzu a Kano, abu ne da ka iya dagulawa ko tarwatsa jihohin Arewa."
"A matsayin mu na gamayyar ƙungiyoyin yaɗa dimokraɗiyya da kishin ta da kuma kare martabar ta, mun ga ya kamata dai mu fito don a ji muryoyin mu don ganin cewa ba mu sa-ido an yi wa al'umma fashi ko ƙwacen abin da su ka zaɓa ba, lamarin da ka iya haifar wa Kano da Arewa baki ɗaya mummunan sakamakon za a yi da-na-sanin afkuwar sa daga baya.
"Mu na ƙara nuni da cewa mu fa ba mambobin NNPP ba ne, kuma ba 'yan asalin Jihar Kano ɗin ne ba ma, amma dai akwai haƙƙi a kan mu da wajibcin fitowa mu yi gargaɗi ga dukkan masu ƙulla wannan kitimirmira da tuggun da a ƙarshe ba zai haifar wa Arewa alheri ba."

A lokacin da ya ke jawabi yayin wani jerin-gwanon lumana ɗauke da kwalaye a 'Tafawa Ɓalewa Tomb', Daraktan Tsare-tsaren CDR mai suna Ibrahim Babayo, ya ce, "Kyakkyawan tsarin dimokraɗiyya shi ne ginshiƙin ɗorewar ƙasa. Kuma abu muhimmi shi ne a kare darajar kowace ƙuri'ar da jama'a suka kaɗa bisa adalci."

Ya ce babban adalci ga kotun zaɓe shi ne ta yi ƙwaƙƙwaran binciken duk wani zargin aikata ba daidai ba a lokacin zaɓe.

No comments

Powered by Blogger.