Header Ads

Yadda Nijeriya Ta Ɗau Saiti Gadan-gadan a Cikin Gida da Waje Ƙarƙashin Mulkin Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya na gabatar da jawabi ga Babban Taro na 78 na Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York a ranar 19 ga Satumba, 2023. (Hoto daga: Frank Franklin II/AP)

Daga Mohammed Idris 

Nan a cikin gida, Shugaba Bola Tinubu ya kama aiki ka'in-da-na'in, ba tare da wani jinkiri ba, musamman manyan tsare-tsaren saita fasalin tattalin arzikin ƙasa.

Baya ga wannan kuma, Shugaba Tinubu ya yi amfani da damar da ya samu a cikin watan Satumba, ya yi wa duniya shiga-da-ƙafar-dama. Satumba ne ya fi zama watan da ayyuka da sha'anin tafiyar da mulki su ka fi kacame masa a cikin duniya, tun bayan rantsar da shi.
Shugaba Tinubu ya na musabaha da Firayim Ministan Indiya, Narendra Modi, a taron ƙungiyar G20 a New Delhi

Shugaba Tinubu ya tafi Indiya inda ya halarci Taron Ƙasashe Masu Ƙarfin Tattalin Arziki na Duniya, wato G20. Shugaban Indiya, Modi, shi ne ya yi masa gayyata ta musamman. 

Daga Indiya, Shugaba Tinubu ya dawo Nijeriya, amma sai da ya yada zango a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya yi ganawa mai muhimmanci da shugabannin ƙasar kan wata matsala wadda ta shafi ƙasashen biyu. Daga can kuma sai Shugaba Tinubu ya nausa taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 78, a birnin New York. Taro ne na shugabannin ƙasashe na duniya, wanda kuma shi ne ya fara halarta a karon farko.

A jawabin Shugaba Tinubu a Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), ya yi bayanai masu ƙarfin gaske, kamar irin dai yadda tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, marigayi Janar Murtala ya taɓa yi shekaru fiye da hamsin baya, inda ya ɗauki hankalin duniya, lokacin da ya riƙa yin kururuwar ƙulla dangantakar cin moriyar juna tsakanin Afrika da duniya baki ɗaya - maimakon yadda manyan ƙasashen duniya suka mayar da Afrika saniyar tatsa ko kuma abin nan da ake ce wa 'kura da shan bugu, gardi da karɓe kuɗi'.

Shugaba Tinubu ya fuskanci shugabannin duniya, ya yi magana a madadin nahiyar Afrika gaba ɗaya, ya taɓo tarihin yadda duniya ta fito da shirin farfaɗo da ƙasashen Turai bayan Yaƙin Duniya na Biyu.

Tinubu ya fara tuna masu yadda shirin 'Marshall Plan' ya taimaka wajen farfaɗo da ƙasashen Turai bayan ragargaza su da aka yi a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu.

Shugaban na Nijeriya kuma Shugaban ECOWAS, Tinubu, ya yi kira ga manyan ƙasashen duniya da cewa "su ƙarfafa dangantakar haɗin gwiwa da Afrika, domin ƙasashen nahiyar su cimma manufar su ta tsayuwa da ƙafafun su nan da shekara ta 2030, sai kuma tabbatar da samun nasarar Cimma Muradun Ƙarni."

A duk ganawar da ya riƙa yi, Shugaba Tinubu ya kan ɗauki tsawon lokaci ya na shaida wa duniya irin tasirin da gwamnatin sa ta samar cikin watanni huɗun sa na farko kan mulki.

Shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen ɗimbin asarar maƙudan kuɗaɗen da Nijeriya ke yi da sunan tallafin man fetur har tsawon shekaru fiye da ashirin. Sannan kuma ya fara yi wa Babban Bankin Nijeriya (CBN) gagarumin garambawul ta hanyar fara jijjige shugabannin bankin da sauran tsare-tsaren da za su yi don ƙara wa tattalin arziki karsashi.

Haka kuma Shugaban ya naɗa ministocin da su ka ƙunshi har da matasa maza da mata masu himma, tare da ƙirƙiro wasu ma'aikatu domin fuskantar ƙalubalen da ke bijirowa a ƙarni na 21.

Idan aka taɓo ƙoƙarin Shugaba Tinubu a Afrika ta Yamma kuwa, a matsayin sa na Shugaban ƙungiyar ECOWAS, Shugaba Tinubu ya nuna himma da jajircewa wajen nuna rashin yarda da katsalandan ɗin sojoji wajen daƙile mulkin dimokiraɗiyya a yankin. Nan da 'yan watanni kaɗan masu zuwa kuwa za a ga nasarar irin ƙoƙarin da ya yi a yankin baki ɗaya.

Shugaba Tinubu na samun cikakken goyon baya da ƙwarin gwiwa daga wurin ministocin sa. A cikin kwanakin da su ka gabata, ni da wasu ministoci mun halarci wani muhimmin taro a Majalisar Ɗinkin Duniya. A wurin taron, na ƙara haƙƙaƙewa dangane da irin himmar da ministocin ke da ita a zahiri wajen ganin an magance matsalolin da su ka addabi Nijeriya.

Zan iya bugun ƙirji da cewa mu na kan dangarama mai tabbatar da cewa tabbas Nijeriya ƙasaitacciyar ƙasa ce a duniya. Ba ni tababar komai kan ministocin Nijeriya da ni kai na a ƙarƙashin jagorancin shugaban mu, Bola Tinubu, cewa za mu cimma muradin ƙara bunƙasa Nijeriya. Daga wannan dangarama da mu ka taka, babu sauran cibaya, sai dai cigaba.

Akwai ayyuka karcat a gaban mu a watanni huɗun nan na ƙarshen 2023. Wannan gwamnati za ta fito da kasafin kuɗin ta na farko, wanda zai zama wata ƙugiyar jawo masu zuba jari da sauran masu son yin haɗin gwiwa da mu. Kuma Nijeriya za ta halarci taron Canjin Yanayi na Duniya (COP28) wanda za a yi a Dubai. A wurin, za mu matsa ƙaimi wajen nuna wa duniya irin muhimman ayyukan cigaba da Shugaban Ƙasa ya fara, kama daga garambawul ga tsarin tara kuɗaɗen haraji da tsarin Bunƙasa Harkokin Gas (CNG), wanda zai sauƙaƙa wa jama'a bayan cire tallafin fetur.

Ko a New York sai da Shugaba Tinubu ya sake jaddada cewa, "Ina sane da halin raɗadin tsadar rayuwa wadda aka shiga bayan bijiro da wasu tsare-tsaren ceto tattalin arzikin Nijeriya. Sai dai kuma duk da haka, ya zama wajibi a ɗanɗani magani mai ɗaci domin mu warke daga cutar da za mu samu sa'ida da ƙarfin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar mu."

A zirga-zirgar da ya yi cikin Satumba ɗin nan, Shugaba Tinubu ya gana da shugabannin Amurka, Indiya, Jamus, Koriya ta Kudu, Afrika ta Kudu, Angola, Jordan da sauran su.

A ɓangaren harkokin bunƙasa kasuwanci kuwa, ya gana da shugabannin manyan kamfanoni irin su Exxon Mobil, Bharti Enterprises, Oracle, Hinduja Group, Indorama, Skipper, Seil da wasu da dama. Sannan kuma an yi masa alƙawurra da alwashin zuba jarin biliyoyin daloli a Nijeriya.

A nawa ɓangaren, ma'aikata ta, wato Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama'a, za ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da samun nasarar wannan gwamnati, kuma za mu yi duk abin da ya wajaba da wanda ya cancanta domin samun wannan nasara. Cikin abin da za mu bijiro da shi har da yadda gwamnatin Nijeriya za ta riƙa mu'amala da 'yan Nijeriya a nan cikin gida da kuma masu zaune a cikin ƙasashe daban-daban.

Nan da kwanaki kaɗan Nijeriya za ta yi bikin cika shekaru 63 da samun 'yanci. Ina da tabbacin cewa irin gagarumar nasarar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta samu abu ne da zai kasance cikin ɗimbin tarihin da zai dauwama a cigaban ƙasar nan.


*Idris shi ne Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai

No comments

Powered by Blogger.