Header Ads

'Yan bindigan daji sun kashe Wakilin 'yan'uwa na Bargi, Neja

A jiya Lahadi 20/08/2023 ne aka tsinci gawar Wakilin 'yan'uwa musulmi na garin Bangi da ke jihar Neja, Malam Abdullahi Umar bayan wasu 'yan bindigan daji sun kashe shi.

Kuma a ranar ta Lahadi aka yi jana'izar Malam Abdullahi Umar, sakamakon kisan da wasu 'yan ta'addan da ba a san ko su waye ba suka yi masa a gonarsa. 

An tsinci gawar marigayin ne kwana daya baya ya bata a jikin wani kwazazzabo a gefen garin Bangi an sassara shi, tare da fasa masa ido daya na hagu.

Wakilin 'yan'uwa na Kontagora, Malam Ibrahim Ahmad Imam ne ya jagoranci yi masa sallar jana'izar da misalin karfe 4:30 na yamma.

Daruruwan jama'a maza da mata ne suka halarci jana'izar, tare da raka shi makwancinsa.

No comments

Powered by Blogger.