Header Ads

'Yan'uwa musulmi a Bauchi sun yi muzaharar Allah wadai da kona Alkur'ani a Sweden

Wani sashen na masu muzaharar a jihar Bauchi

Almajiran shugaban harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, na Da'irar Bauchi da kewaye maza da mata sun gudanar da muzahara domin yin Allah wadai da kona Alkur'ani da aka yi a kasar Sweden.

An gudanar da muzaharar ne da safiyar ranar Litinin bayan an sanar da haduwa domin gudanar da ita a makarantar Fudiyya Bauchi a ranar Lahadi. 
Muzaharar ta gudana ne a karkashin jagorancin wakilin 'yan uwa na jihar Bauchi, Sheikh Ahmad Yashi.

No comments

Powered by Blogger.