Header Ads

'Yan'uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzaky a Potiskum sun gabatar da muzaharar Allah wadai da kona Al-Kur'ani a Sweden

'
Wani sashe na wadanda suka gabatar da muzahara a garin Potiskum domin yin Allah wadai da kona Alkur'ani da aka yi a kasar Sweden

Almajiran shugaban harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, da ke garin Potiskum sun gabatar da muzahara domin yin Allah wadai da kona Alkur'ani mai tsarki da aka yi a kasar Sweden.

An gabatar da muzaharar ta ne a ranar Juma'a, 7 ga watan Yuli na shekarar 2023 wanda ya yi daidai da 18 ga watan Dhul Hijja, 1444 bayan hijira.

Biyo dai bayan kona Alkur'ani mai tsarki da wani mutum, Salwan Momika, mai shekaru 37 ya yi a ranar Eid Al-Adha a kusa da babban masallacin Stockholm da ke Sweden, Musulmai da dama da ke kasashen duniya suna ta gudanar da zanga-zanga domin yin Allah wadai da al'amarin, ciki kuwa har da Nijeriya inda aka gudanar da muzaharori a garuruwa da suka hada da Kaduna, Kano da Bauchi. 

Kasashe da dama sun yi Allah wadai da kona Alkur'ani da aka yi wadanda suka hada da Saudi Arabiya, Turkiyya, Iran, Iraki, Kuwait, Moroko da sauransu.

No comments

Powered by Blogger.