Header Ads

Yadda Wasan Kwaikwayon ’Yan Gwagwarmaya Ya Kawo Sauyi A Kasashen Larabawa

  

Daga Dakta Abou Jawad

 

Silma da wasan kwaikwayo (dirama) sun mamaye gurbi mai girma gun kowa da kowa, kuma masu kallo da sauraro suna biye da shi, kuma kayan aiki ne mai muhimmanci wanda za a iya amfani da shi ta hanyar gaskiya ko kuma maras kyau, kuma ayyukan gwagwarmaya suna da kyau ga mai kallo. Kuma saboda waɗannan dalilai mun ga yadda ake gudanar da tarukan karawa juna sani na nazari kan batutuwa daban-daban a fima-fimai. Kamar dai yadda a baya-bayan nan aka gudanar da wani taron karawa juna sani mai taken: "Dirama ta gwagwarmaya a Labanon… Matsaloli da Magani" a gaban masana da masu binciken fasaha, ciki har da dan kasar Labanon din nan  manazarcin fima-fimai kuma mai bincike a cikin nazarin fasaha, Dk. Husain Samaha, wanda ya sami kwarewa mai kyau a fannin horo, ilimi, da kuma yin fim, kuma ya yi aiki tare da babban Darakta, Shahidi Husain Abdullah, kuma ya yi aiki da Mu'assasar "Foundation Inheritance" don samar da fasahar da ke da alaka da abin da ya shafi shahidai. Yana fassara fima-fimai da silsila da dama, ya kuma shiga fima-fimai da dama. Yana da kwarewa sosai a fannin fasaha, don haka muka yi amfani da damar da muka samu muka tattauna da shi Dk. Samaha game da wasan kwaikwayo.  Ga rubutun tattaunawar:

 

SHIRIN DIRAMA NA LARABAWA

 

Da farko dai mun nemi Dakta Samaha da ya bayyana ra'ayinsa da kimanta wasan kwaikwayo a kasashen Larabawa, sai ya ce: Ba tare da la'akari da kwatance na musamman da za a iya gabatar da shi ga shirya fima-fiman Larabawa ba, da kuma ko ya bi tsarin yin fim da duniya ta amince da shi ba da kuma layin samar da shirye-shiryen talabijin a matsayin wanda za a kimanta shi a kimiyyance, ba karin gishiri ba ne in aka ce shirin wasan kwaikwayo na Larabawa yana fama da matsaloli da dama wadanda suka bambanta kan tsanani daga kasa zuwa kasa da kamfanonin da ke kula da harkar, duk da fitar da kusan dala biliyan daya da aka kashe a wasan kwaikwayo na Larabawa a cikin shekarar da ta gabata. Yaduwar dirama na kasashen waje (musamman Turkiyya da Mexico) a kasashen Larabawa ya yi tasiri matuka wajen zana taswirar dirama na Larabawa.

 

Dalla-dalla, ana iya cewa wasan kwaikwayo na Masar yana fama da matsalar wasu manyan kamfanoni masu zaman kansu na shirya wasan kwaikwayo sun yi babakere a masana'antar, yayin da sauran kananan kamfanoni suka gamsu da zama karkashin su wajen samar da fima-fiman. Don haka, waɗannan manyan kamfanoni sun sami damar rungumar ma'aikata a cikin wasan kwaikwayo, ciki har da masu fasaha, kuma sun dauki kafofin watsa labaru na Masar a matsayin dandalin su don tallata ayyukansu.

 

Wannan al'amari ya haifar da yanayi na kashin kai ko na yau da kullum a cikin samar da fima-fimai, nesa da ma'anar gasa da wasan kwaikwayo na Masar a baya ya shaida tare da takwarorinsa na kamfanoni da sauran kasashen Larabawa. Wannan katsalandar dai ta shafi Balarabe mai kallon wasan kwaikwayo na Masar a matsayin wata hanya gare shi da kuma tagar ilimi da nishadi a lokaci guda, wanda hakan ya sa ya nemi wani zabin.

 

Daga nan ne gidajen Talabijin masu zaman kansu suka fito daga tsarin wajibcin samar da fima-fiman Larabawa zalla, don taka rawa wajen dinke gibin da ya samu ta hanyar Larabtar da ayyukan fima-fiman Turkiyya da na Mexiko, don gujewa babakeren da manyan kamfanonin ke haifarwa a kan samar da fima-fiman.

 

Wannan sassaucin da aka samu wajen sauya sheka daga asali na fima-fiman Larabawa zuwa wasan kwaikwayo na Larabawa ana daukar sa a matsayin takobi mai kaifi biyu sakamakon ra'ayoyi daban-daban da za su iya kutsawa cikin yanayin Larabawa da kuma girman tasirinsu mai kyau ko mara kyau. Amma fa wannan batu ne da ke wajen maudu'in tattaunawar mu ta yanzu.
DIRAMA A LABANON

Dakta Samaha ya ci gaba da cewa: Dangane da kasar Labanon kuwa, duk da irin koma bayan da wasan kwaikwayo na kasar Labanon ya yi a lokacin yakin basasa, bayan Beirut ta kasance babban birnin gidajen kallon fima-fiman Larabawa, kuma cibiyar raya fima-fiman Larabawa (tare da Alkahira), kuma bayan dogon suman da wannan wasan kwaikwayo ya shaida tun lokacin da Isra'ila ta mamaye Labanon, karshen yakin basasar a shekarun tis'inoni, wannan wasan kwaikwayo ya sami damar tashi ta hanyar wasu kamfanoni da ayyukan shirye-shiryen fima-fimai, waɗanda ba su kai matakin yaɗuwa zuwa kasashen Larabawa da na duniya ba, amma sun kasance takaitattu ga kasuwar Lebanon, har ya zaman hoton wasan kwaikwayo na ainihi na Labanon ya kasance a takaice da wasu sunaye irin su: Nadine Labaki, Georges, Khabbaz, da sauransu.

 

Bayan 2011 kuma tare da farkon rikicin siyasa, soja, da tsaro na Siriya, da kuma sakamakon babban gudun hijirar 'yan Siriya zuwa yankunan Lebanon, masu sana'ar dirama na Siriya sun zama wani muhimmin bangare na wannan kaura, wanda ya tilasta fitowar ayyukan haɗin gwiwar 'yan Siriya da Labanon. Wannan hadaka ta abubuwan fasaha na Lebanon da Siriya sun ba da gudummawa ga gagarumin farfadowa na wasan kwaikwayo na Labanon, kuma ya karfafa bangaren Labanon don tafiya ta hanyar kwarewa na kamfanoni na Lebanon masu zaman kansu waɗanda ke da burin samar da fima-fiman Lebanon zalla, tare da cikakken ikon 'yan kasar, amma tare da zurfin kwarewar Larabawa da kasashen duniya.

 

WASAN KWAIKWAYO A KASASHEN YAKIN TAKEN FASHA

 

Dk. Samaha ya kara da cewa: Dangane da wasan kwaikwayo a kasashen Yankin Gulf na Farisa, duk da tafiyar hawainiyar da hakan yake shaidawa, mun ga cewa wannan wasan kwaikwayo ya iya samo kyakkyawan tsari na gaba daya a cikin samar da fima-fiman, amma ba a abin da ya kunsa ba, ta hanyar kasafin kudi masu yawa da aka kashe a kansa wajen samarwa, daukar hoto, yin ado da sauran abubuwan samar da fima-fimai ingantattu.

 

Wannan ya bayyana a wasu shirye-shiryen fima-fiman Saudiyya na baya-bayan nan, wadanda suka shahara sosai a wurin masu kallo a kasashen yankin Gulf na Farisa (Fim din "Sattar" ya sami mafi girman kudaden shiga a cikin kasashen Larabawa), sabanin abin da ya shahara a cikin 'yan shekarun nan na ce-ce-ku-ce tsakanin wasan kwaikwayo da masu kallo a kasashen yankin GULF NA FARISA.

 

A bayyane yake cewa wasan kwaikwayo a cikin kasashen Gulf na Farisa yana fama da mummunar matsalar rubutu. Hasali ma, da alama da wuya a iya gano marubucin da ya bar wani tasiri mai karfi a wasan kwaikwayo na ƙasashen Gulf na Farisa da kasashen Larabawa. To, sai dai kuma masana daga wadannan kasashe na ganin cewa, nan gaba ba za a yi kasa a gwiwa ba, sai dai akwai kyakkyawan fata a tsakanin masu fasahar kirkiro dirama, ganin yadda akwai  kwararru da za su iya karkatar da gibin da ke akwai na wasan kwaikwayo a kasashen Gulf na Farisa a nan gaba, don sanya shi a cikin jerin wasan kwaikwayo na Larabawa.

 

WASAN KWAIKWAYO A SIRIYA

 

Dk. Samaha ya tabo wasan kwaikwayo na kasar Sham, inda ta kalamansa, ya ce: A daya bangaren kuma, har yanzu wasan kwaikwayo na kasar Sham yana kan gadon sarautar mafi yawan al'ummar Larabawa, musamman a lokacin da ake gudanar da gasar tseren Ramadan a kowace shekara, duk kuwa da yakin duniya da ake fama da shi a kasar. Kuma ana yaba wa Siriyawa saboda yadda suka iya cilla wannan motsin sama na wasan kwaikwayo a ƙasarsu, duk da mummunan yanayin da suke ciki.

 

Ba boyayye ba ne cewa irin ci gaban da wasan kwaikwayo na kasar Sham ya samu a adadi da inganci, da yadda yake jawo fuskar Larabawa, a dalilin bambancin batutuwan da ake da su ne a fima-fiman, da kuma daukar matakan aiwatar da su da kuma samar da su cikin inganci. Haka nan kuma, dandalin wasan kwaikwayo na kasar Sham ya shaida rashin gamsuwa da wasu muhimman sunaye a cikinsa, inda suka yi suka kan sakamakon hanyoyin da wasu ba su so, tare da la'akari da wadannan hanyoyin a matsayin wata dama ta mamayar da fitattun kamfanoni da masana'antu suka yi tare da kashewa tare da dakile sababbin kamfanoni, abin da ke fayyace irin matsalar da wasan kwaikwayo na Masar ke fama da shi.

 

Bugu da kari, ana iya cewa yada wasan kwaikwayo na Turkiyya ya iya fitar da duk wani karsashi daga dimbin hasken ayyukan fima-fiman kasar Siriya, bayan da jerin shirye-shiryen Turkiyya suka yi matukar farin jini a wajen masu kallo Larabawa, lura da cewa kamfanonin da ke samar da fima-fiman na kasar Siriya sun yi fice sosai, kuma na farko da suka fassara da kuma yi wa jerin shirye-shiryen fima-fiman Turkawa fassara, wanda ya yi aiki wajen inganta su sosai. A baya-bayan nan, wasan kwaikwayo na Turkiyya ya tabbatar da matsayinsa a kasashen Larabawa har ya kai ga gudanar da ayyukan hadin gwiwa tsakanin Siriya da Turkiyya, kuma hakan ya kara karfafa gwiwa da mu'amalar da masu kallo Larabawa suka yi da wasan kwaikwayo na Turkiyya.

 

WASAN KWAIKWAYO NA GWAGWARMAYA

 

Da muka tambayi mai girma Dk. Samaha game da siffofin wasan kwaikwayo na gwagwarmaya da shirye-shiryen samar da su a wannan fanni, sai ya amsa mana da cewa: A halin yanzu yana da wuya a yi magana game da wasan kwaikwayo na gwagwarmaya, a ma'anar cewa shi ma wani nau'i ne mai zaman kansa kamar sauran nau'o'in fima-fimai irin su fima-fiman tsoro, fada, almarar kimiyya, wasan barkwanci, da sauran nau'o'in fima-fimai da aka sani. Kwanan nan, duk da haka, jerin wasu fima-fimai da wasan kwaikwayo sun fito waɗanda suka ɗauki batun gwagwarmaya a matsayin jigon abubuwan da suke cikin fima-fimansu. An kuma fitar da su a karkashin taken wasan kwaikwayo na gwagwarmaya, amma ba su kunshi abubuwan da suka bambanta da sauran nau'ikan da za a bambanta su ba, ba a cikin fim ko a cikin ba da umarni ko a cikin wasu abubuwan ban mamaki ba, wanda ke siffanta kowane ɗayan waɗannan nau'ikan.

 

Har ma a iya cewa akwai cakudewar sifofin wasu nau'ikan a ciki. A cikin bayanin abubuwan da suka shafi wannan salon, yana yiwuwa a ga kyakkyawan dandano na zamantakewa wanda ke ba da labarai daga yanayin gwagwarmaya, wasu na jin daɗi, shakku, fada, da yaki, tunda muna magana ne a kan batun tunkarar makiyiya Isra'ila ta hanyoyin soji da tsaro tun da farko.

 

Tun daga farkon shekarun tis'inoni, harkar gwagwarmaya ta fara kunna fagen samar da fima-fimai saboda fahimtar da take da shi na shiga ayyukan yaki ruwan sanyi, da isar da gaskiya, da kuma janye kafafun makiya, wadanda suka fara karyata gaskiya da yada karerayi da wuri da nufin haifar da baraka tsakanin masu gwagwarmaya da sauran jama'a.

 

Masu kallo kodayaushe sun kasance, kuma har yanzu wani muhimmin bangare na daidaiton gwagwarmaya, daukar nauyi da samun nasara, kuma mafi mahimmanci shi ne cewa labarun da aka yi a cikin wasan kwaikwayo na gwagwarmaya wani bangare ne kawai na tarihin dukkan batun, a lokacin da ake ɗaukar wasan kwaikwayo a matsayin hanya mai tasiri wajen rubuta tarihi a cikin sauti da bidiyo daidai da rubuta shi ta hanyoyin gargajiya.

 

Daga nan ne sai gwagwarmaya ta cike guraben da ke kan karami da babban allon kallo da sauri, kuma a lokaci guda, in ba haka ba da makiya za su iya cike wannan gurbin ta yadda suka ga dama, wanda ake ganin abu ne mai hatsarin gaske. Don haka fagagen Lebanon da na Palastinawan sun ga wani yunkuri na ban mamaki, amma bai kai matakin da ya kamata ba tukun. Jama'a na jiran ta ne ta hanyar da ta dace da nasarorin da mayakan gwagwarmaya suka samu a fagen daga. To, sai dai kuma wadanda ke da alhakin gudanar da wannan aikin sun himmatu wajen raya irin wannan wasan kwaikwayo bisa ga iyawar da ake da su, kuma a kan haka za a iya cewa, muna ganin an samu gagarumin ci gaba ta fuskar tsari da abin suka kunsa da kuma iya aiki kowace shekara tare da dukkan gibin da ake da shi, wanda za a iya magana a kai a nan gaba.

 

Daga cikin wadannan shirye-shiryen, za mu iya ambaton jerin silsilan dirama na Labanon, ciki har da: "Masu Nasara" kashi na farko da na biyu, "Tashin Bindiga", "Malt al-Turab", "Bouh Al-Sanabel" da sauransu, da kuma jerin silsilan fima-fiman Palastinawa da suka hada da: “Al-Fida'i” kashi na farko da na biyu, “Kofar Sama”, “Shara Nasr Gilboa” da sauransu.

 

Bugu da kari, duk wannan, ba zai yiwu a yi watsi da nau'in fim ɗin juriya ba wanda matakin fasaha da sana'a ya bambanta bisa ga iyawa da kasafin kuɗi da aka kashe a kai, amma masu sauraron juriya sun yaba da shi sosai. Hasan Abdullah, da kuma fim din "Khalet Warda" na darektan Lebanon "Adel Sarhan" da kuma fim din "Mutanen Wafa" na darektan Syria "Najdat Anzour", wadanda gaba daya cibiyoyin gwagwarmaya a Lebanon suka shirya su.

 

FINA-FINAN HADIN GWIWA NA IRAN DA LEBANON

 

Dk. Samaha ya ci gaba da cewa: Har ila yau, za a iya yin magana kan wani bakan na fima-fiman hadin gwiwa na Iran da Lebanon da suka dauki gwagwarmaya a Lebanon da Palastinu a matsayin abubuwan da suka kunsa, wadanda aka nuna su a zauruka kallo na babba da karamin allo, wadanda suka shahara sosai ga masu kallon da aka nufa. A cikin su mun ambaci fim din nan mai tasiri, wanda aka yi la'akari da shi a zamaninsa, kuma fim ne shahararre mai suna “The Remains” wanda “Saifullah Dad” na Iran ya ba da umarni, kuma “Ghassan Kanafani” ya rubuta a 1994.

 

Bugu da kari, za a iya ambaton wadannan fima-fimai: "Hiyam", "Jarh Al-Zaytoun", "A New Birth", "33 Days", "A Chord of Calories", da kuma fim din "Abu Zainab", wanda ya ba da labarin Shahidi Amer Kalakish a cikin kyakkyawan tsari mai ban mamaki.

 

RAWAR YAKI A KAFAFEN YADA LABARAI NA IRAN DA LABANON

 

Dangane da manufofin wasan kwaikwayo na gwagwarmaya da samun sa, ko matsaloli da mafita a wannan fage, Dk. Samaha ya ce: Wasan kwaikwayo, wanda ke daukar gwagwarmaya da makiyiya Isra'ila da kuma rikici tsakanin turakun gwagwarmaya da ayyukan kasashen Yamma a yankin a matsayin takensa, ya sami damar cimma muhimman buruka duk da gibin da yake fama da shi, tun daga farkonsa a cikin shekaru tis'inoni na karnin da ya gabata. A bayyane yake cewa jagorancin gwagwarmayar ya gindaya makasudi mai muhimmanci a gare shi, wanda ya zama dalilin da ya sa ya fara zabin yin kwaikwayon labarun gwagwarmaya ta hanyar wasan kwaikwayo. Waɗannan burin sun fito ne a kan gatura guda uku:

 

1- Yakin ruwan sanyi, karyata tunanin makiya da fuskantar farfagandarsa ta karya.

 

2- Aike da sako zuwa ga muhallin gwagwarmaya a matsayin ginshikin arangama, da nufin karfafa azama, yada gaskiya, gyara tunani, da hana kutsawar makiya.

 

3- Aika sako zuwa ga kafafen yada labarun kasashen makiya.

 

Kafofin yada labaran yaki a gwagwarmayar Palastinu da Lebanon sun taka rawar gani a ci gaba da yakin da suke yi da sahyoniyawan makiya ta hanyar daukar hotunan soja, tsaro da sauran ayyukan gwagwarmaya, da watsa su a kafafen yada labarai na cibiyoyin gwagwarmaya. Kuma ya kasance har yanzu yana kai wa ga mafi girman bangare na al'ummomi daban-daban, musamman bayan yaduwar al'amuran dandalin sada zumunta. Da ma dandalin sada zumunta da kafofin watsa labaru na soja sun kasance koyaushe suna daidai da sauran cibiyoyin watsa labaru, ciki har da tashoshin talabijin, gidajen wasan kwaikwayo (duk da karancin su), gidajen rediyo, da jaridu.

 


WASAN KWAIKWAYO BISA NASARORIN DA AKA SAMU NA GWAGWARMAYA

 

Dk. Samaha ya kara da cewa: Kodayake a baya-bayan nan wasan kwaikwayo ya mamaye wani muhimmin matsayi, don haka tilas ne gwagwarmaya ya kai wannan fagen don karyata ra'ayin makiya tare da tunkarar farfagandarsa na karya, wanda ta hakan ne a kodayaushe yake neman karkatar da gaskiya da wasa a kan wannan batu na nuna martabar gwagwarmaya da daukarsa a matsayin wani nau'i na ta'addanci da kuma karfafa ra'ayin ficewa daga dokokin kasa da kasa, tare da daukar Mujahidai a matsayin gungun matasa masu zullumi da jajircewa wadanda ke kai al'ummarsu zuwa ga rami saboda rashin daidaito da rashin yiwuwar fuskantar dakaru a matakin sojojin makiya Yahudawan sahyoniya ta fuskar kayan aiki da adadi da matakin ilimi da sauran kura-kurai da makiya suke neman yadawa a cikin al'ummomin Larabawa da na Musulunci don tabbatar da hakan a matsayin hujjar da ba za a yi watsi da ita ba bisa ka'idar cewa; “Ido ba zai iya turjiya da mujiya ba.”

No comments

Powered by Blogger.