Yadda Ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Nijeriya ya gudanar da bukin Eid al-Ghadeer
Wani sashe na mahalarta taron Eid al-Ghadeer wanda ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Nijeriya ya shirya.
Ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke Abuja ya gudanar da bukukuwan Eid al-Ghadeer a ranar Laraba, inda jakadun kasashen Lebanon, Siriya da Iraki suka halarta bayan masana da malamai da suka halarci taron daga Nijeriya.
Eid al-Ghadeer ana daukar sa a matsayin babban biki a Musulunci, musamman ga mabiya Ahlulbayt (as). Ita ce ranar Manzon Allah Muhammad (S) ya nada Imam Ali bin Abi Talib (AS) a matsayin kalifansa a ranar 18 ga watan Zhul-Hijjah.
Kamar yadda kafar watsa labarai ta Iran Press ta ruwaito, yayin bikin da aka gudanar a ofishin jakadancin na Jamhuriyar Musuluncin ta Iran a Abuja, Kari na Iran, Amin Hassani, ya bude taron da karanto ayoyi daga cikin Alkur'ani mai tsarki.
Ambasadan Iran a Nijeriya, Mohammed Alibak, ya yi magana akan muhimmancin Eid al-Ghadeer inda ya kammala jawabinsa da yin Allah wadai da keta alfarmar abubuwa masu tsarki na Musulunci da Sweden ta yi, wanda ya fusata duniya Musulmai.
"Menene ma'anar 'yanci? 'Yanci ne mutum ya ci mutuncin abubuwa masu tsarki da addini? Addinin Musulunci bai bari kowa ya ci mutuncin addinin wani ko imaninsa ba. Wadannan ayyuka an yi Allah wadai da su kuma gwamnatoci bai kamata su kyale kowa ya ci mutuncin addinin mutane ko imaninsu ba." Kamar yadda Alibak ya bayyana.
Kamar yadda ya ke a cikin rahoton, Sheikh Umar Abubakar Kumo daga jihar Gombe wanda shine shugaban "Ahlulbayt Muslim Community in Nigeria" yayin da ya ke yin jawabi, ya bayyana yadda Manzon Allah Muhammad (S) ya samar da makarantar Ghadeer: "Imam Ali shine mai kula da Musulunci. Shine mai kariya ga addini."
Dakta Yusha'u, wanda shine wakilin shugaban harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Zakzaky, a wajen bikin Ghadeer din, shima an ba shi dama domin yin jawabi dangane da yadda aka nada Imam Ali bin Abi Talib a matsayin shugaban Musulmai na farko.
Post a Comment