Header Ads

Yadda aka yi juyayin Ashura a Barcelona da ke Spain

Ranar 10 ga watan Muharram babbar ranar ce wadda Imam Hussain (as) da sahabbansa suka nuna sadaukarwa a Karbala. Kamar yadda ya ke a sauran wurare a duniya, a garin Barcelona da ke kasar Spain nan ma an gudanar da juyayin Ashura.

Kamar yadda ya ke a cikin wani rahoto na kafar watsa labarai ta Iran Press, an fara gudanar da juyayin Ashurar ne a Barcelona daga cibiyar Wilayat Imam Bargha Al-Ka'im da ke Barcelona din inda aka tafi zuwa Plaza R. de Tanif.

Kamar yadda kafar ta bayyana, musulmai a baki daya kasar ta Spain sun shiga cikin juyayin kuma sun nuna biyayyar su ga jikan na Manzon Allah (S) a yayin da kuma malamai suka yi bayani dangane da koyarwa bisa gaskiya da ke cikin al'amarin da kuma gaskiya irin ta Hazrat Imam Hussain (as) da sauran al'amurran da suka shafi waki'ar da ta afku a Karbala.

No comments

Powered by Blogger.