Header Ads

Yadda aka yi bukin tunawa da ranar haihuwar Imam Mousa Kazim (AS) a Mashhad

Haramin Imamai biyu, Imam Mousa Kazim (AS) da Imam Muhammad Al-Jawad (AS), Imamai na bakwai da na tara, a garin Al-Kadhimiya da ke arewa da Baghdad, kasar Iraki

Mutanen kasar Iran sun yi bukin tunawa da ranar haihuwar Imam Mousa Kazim (AS), Imami na bakwai a Shi'a, ciki har da a Mashhad da ke arewa-maso-gabashin kasar Iran.

Ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli, shekar 2023 ita ce ta yi daidai da 20 ga watan Dhul al-Hijja, ranar da aka haifi Imam Mousa Kazim (AS).

Mutane sun ziyarci haramin Imam Reza (AS) domin bukin ranar haihuwar Imamin na bakwai na Shi'a.

An san Imam Kazim (AS) sosai saboda kamun kan sa, gaskiya, kyautatawa da kuma matukar hakurinsa da taimako ga wadanda suka bata masa, an yi masa lakabin "Kazim" ne saboda hadiye fushinsa.

Bayan shahadar mahaifinsa, Imam Jafar Sadik (AS), Imam Kazim (AS) ya dauki nauyin nuna shiriya ga al'ummar Musulmai.

Haramin Imam Kazim (AS) yana a Kadhimiya ne, arewa da Baghdad babban birnin kasar Iraki.

No comments

Powered by Blogger.