Header Ads

UNIJOS, ta kara kudin makaranta daga naira 45,000 zuwa sama da naira 200,000

Jami'ar Jos, UNIJOS, ta bayyana karin kudin makaranta daga yadda ya ke a naira 45,000 zuwa naira 213,000, wanda hakan ke nuni da kari na sama da kashi 300 a cikin dari.

Kamar yadda sabon jadawalin biyan kudin makaranta na makarantar ya nuna wanda rijistira na makarantar ya sawa hannu, kudin makarantar na naira 213,000 ga 'yan aji daya ne da aji biyu a jami'ar, yayin da 'yan aji uku zuwa sama a yanzu za su biya naira 160,000, kamar yadda ya ke a cikin wani rahoto na kafar watsa labarai ta Sahara Reporters.

kafar dama ta yi rahoton cewa a shekarar 2017 jami'ar ta kara kudin makaranta daga naira 27,000 zuwa naira 45,000.

Shugaban jami'ar na wancan lokacin, Farfesa Sabastian Maimako, ya bayyana dalilan rashin samar da isassun kudade, hauhawar kashe kudade da kuma bukatar inganta wasu abubuwa.

Kafar ta Sahara Reporters ba ta iya tabbatarwa nan da nan ba ko shugaban jami'ar na yanzu, Farfesa Tanko Ishaya, ya samu daidaito da kungiyoyin dalubai, gwamnati, iyaye da masu ruwa da tsaki ba kafin irin wannan babban kari ga kudin makarantar.

Karin kudin makarantar ta UNIJOS na zuwa ne sati daya bayan jami'ar Legas (UNILAG) ta bayyana karin kudin makaranta wanda hakan ya sa iyaye da 'yan Nijeriya kin amincewa da karin kudin makaranta da jami'o'i ke yi a fadin kasa. 

'Yan tafiyar Take-It-Back sun bayyana karin kudin da jami'o'i ke yi a halin yanzu a fadin kasa a matsayin abinda ke cikin "sabon tsarin" gwamnatin da Tinubu ke yiwa jagoranci a yayin da miliyoyin 'yan Nijeriya ke cikin halin talauci.

"Ta hanyar bin sabon tsarin gwamnatin @officialABAT da ke da niyyar fitar da kudin ilimi daga talakawa, mahukuntan jami'ar @UnilagNigeria da sauran makarantu sun yanke hukuncin yin babban kari ga kudaden makaranta.

"Wannan na zuwa ne a yayin da 'yan Nijeriya sama da miliyan 150 ke cikin talauci wanda ya kara ta'azzara sakamakon wahalhalun da ba a taba samu a baya ba sakamakon karin kudin man fetur da kuma kudin wutar lantarki. 

"Muna tare da daluban jami'ar Legas, iyaye talakawa da miliyoyin dalubai 'yan Nijeriya wadanda wannan sabon tsari a kan ilimi a kasa zai shafa." Kamar yadda TIB ta bayyana.

No comments

Powered by Blogger.