Header Ads

Tarayyar Turai ta yi Allah wadai da kona Al-Kur'ani a Sweden, ta bayyana shi da "Cin mutunci, rashin girmamawa"

Zauren Majalisar Tarayyar Turai 

Tarayyar Turai (EU) da kakkausar murya ta yi Allah wadai da kona Alkur'ani da aka yi a 'yan kwanakin nan a kusa da babban masallacin babban birnin kasar Sweden, Stockholm, inda ta kira hakan da "a fili ya ke tonon fada ne." 

A cikin wani jawabi a ranar Asabar, tarayyar ta EU ta ce wannan al'amari na "cin mutunci da rashin girmamawa" ba ya yin nuni da ra'ayin tarayyar, inda ta bayyana cewa "nuna wariya, kiyayyar baki da abubuwan da suka shafi rashin iya zama da wasu" ba su da matsugunni a nahiyar Turai, kamar yadda kafar watsa labarai ta Press TV ta ruwaito.

Ta kara da cewa tarayyar na girmama 'yancin yin addini ko imani da kuma 'yancin fadar albarkacin baki a cikin kasashen da ke kungiyar da kuma sauran kasashen duniya.

Jawabin ya kara da tabbatar da cewa "Yanzu lokaci ne na zaman tare domin a fahimci juna da girmama juna da kuma hana faruwar wani abu a gaba." 

Al'amarin cin mutunci ne musamman ma da yake ya faru ne a lokacin da musulmai suke yin bukukuwan Eid Al-Adha.

Tarayyar ta ma nuna rashin amincewarta da kutsawa cikin ofishin jakadancin kasar Sweden da aka yi a babban birnin kasar Iraki, Baghdad, kamar yadda ya ke a cikin jawabin.

A dai ranar Laraba ne wani dan kasar Iraki mai shekaru 37 ya taka Alkur'ani sannan ya sawa shafukansa da dama wuta a kusa da babban masallacin da ke Stockholm. Wannan cin mutunci ga littafi mai tsarki na Musulmai an yi shi ne karkashin yarda da kariyar 'yan sandan Sweden.

Wannan al'amari, wanda ya faruwa lokacin da ake gudanar da Eid Al-Adha bayan kammala aikin Hajji a Makkah da ke Saudi Arabiya, ya bakanta ran Musulmai a fadin duniya.

A ranar Juma'a, dubunnan 'yan kasar Iraki sun taru a rana ta biyu a jere domin yin zanga-zanga dangane da kona Alkur'ani da aka yi Sweden.

Mutane a sauran kasashen musulmai su ma sun hau kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da al'amarin.

Kungiyar Kasahen Musulmi (OIC) ta gudanar da taron gaggawa na kwamitin zartarwarta domin kawo mafita dangane da mummunan al'amarin.

Kasar Sweden akai-akai ta sha kyalewa a kona Alkur'ani a cikin shekarun nan. A cikin watan Janairu, wani dan kasar Denmark a Sweden mai tsatstsauran ra'ayi ya kona Alkur'ani kusa da ofishin jakadancin Turkiyya a da ke Stockholm.

No comments

Powered by Blogger.