Header Ads

Sufeto Janar na 'yan sanda ya kira wasu 'yan sanda Abuja bayan sun bi ta kan wani mutum da mota

Mutumin da 'yan sanda suka bi ta kan sa da mota yayin da ya ke kwance a gaban motar sintirin ta 'yan sanda


Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya mai rikon kwarya, Kayode Egbetokun, ya yi Allah wadai da wani al'amari da ya faru inda wasu 'yan sanda suka bi ta kan wani dan kasa da mota a ranar Alhamis, 29 ga watan Yunin 2023.

Ya bayar da umarnin cewa 'yan sandan da suka yi laifin, wadanda ake tsare da su a jihar Edo, da su zo cibiyar rundunar a da ke Abuja domin daukar mataki na gaba.

Wani jawabi daga jami'i mai hulda da jama'a na hukumar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya kara da cewa, "Jama'ar kasa, musamman mutanen Ekpoma, ana neman da su kwantar da hankalinsu domin shugabancin hukumar 'yan sanda (NPF) na yanzu ba zai amince da wannan rashin iya aikin da rashin kwarewar ba." 

Kafar watsa labarai ta Sahara Reporters a ranar Juma'a ta ruwaito cewa Adejobi, wanda ya yi mamaki a kan faruwar al'amarin, ya ce rundunar ya kamata ta dauki mataki nan take. Ya ce ya yi magana da kwamishinan 'yan sandan jihar.

A cikin bidiyon mara kyan gani, an ga wani mutum sanye da ankwa kuma 'yan sanda sun murkushe shi a cikin wata karamar mota a Ekpoma da ke jihar Edo. 

A cikin bidiyon, an ga wani mutum a kwance a gaban motar sintiri, mutanen yankin sun zo suna yiwa 'yan sandan magana, sai kawai wani a cikinsu da ya ke tuka motar ya fara tuka motar ya murkushe mutumin yayin da taya daya ta bi ta kansa, sai daga bisani ne ya tsayar da motar yayin da mazauna yankin ke ihun cewa akwai mutumin a kasan ta.

Yayin da ya ke magana a kan al'amarin, Adejobi ya bayyana cewa ya kasa amincewa a ce wai mutum mai hankali zai murkushe mutum da mota ba ma wai kawai jami'in tsaro ba.

"Ba haka aikin dan sanda ya ke ba. Ba na tunanin mutum mai hankali zai yi haka. A murkushe mutum da mota? Wannan ba abu mai faruwa bane. Da kai na, na kira kwamishinan 'yan sandan jihar Edo a kan wannan al'amari. Ya kamata mu dauki matakin gaggawa a kan al'amarin. Ni kam abu ne mai ban mamaki a matsayi na na mutum." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin.

A yanzu haka dai, mutumin da aka murkushe da motar yana asibitin kwararru na Irrua da ke jihar Edo yana jinya kamar yadda wanda ya wallafa bidiyon ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.