Header Ads

Sudan na gaf da fadawa cikin yakin basasa - Majalisar dinkin duniya

Wasu sojojin Sudan da ke yin biyayya ga shugaban sojoji, Abdul Fattah al-Burhan, a zaune a kan wata tankar yaki a birnin Port Sudan da ke bakin tekun Red Sea a ranar 20 ga watan Afirilun shekarar 2023.

Rikici a kasar Sudan da ke fama da rikice-rikice na gaf da zama "na yakin basasa," wanda zai iya hargitsa baki daya yankin, kamar yadda Majalisar dinkin duniya ta bayyana a ranar Lahadi, bayan wani harin jiragin sama a gidan da mutane suke da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane kusan 20.

Ma'aikatar lafiyar kasar ta yi ikirarin cewa, "mutane 22 suka rasu kuma fararen hula da dama sun raunata" daga harin wanda aka yi a birnin Omdurman da ke kusa da babban birnin kasar, Khartoum, a yakin Dar al-Salam, wanda ke nufin "Gidan Aminci" da Larabci. 

Harin jirgin saman na zuwa ne kusan watanni uku bayan fada da ake yi a tsakanin janarorin kasar ta Sudan da ba su shiri. 

Kusan dai mutane 3,000 duka rasa rayukansu sakamakon yakin; wadanda suka tsira sun bayyana cewa akwai hauhawar cin zarafi, kuma shaidu sun yi magana a kan kisa na kabilanci. Ana yin sace-sace a ko'ina, kuma majalisar dinkin duniya ta yi gargadin aikata laifuffuka a kan bil-adama a yankin Darfur.

Ma'aikatar lafiyar ta wallafa wani bidiyo a kafar sada zumunta ta Facebook da ke yin nuni da wadanda suka rasu sakamakon harin, inda ya shafi 'yan mata masu yawa. Kamar yadda mai yin jawabi ya bayyana, mazauna "sun kirga mutane 22 da suka rasu," kamar yadda kafar watsa labarai ta PM News ta ruwaito.

Mayakan RSF, wadanda ke fada da sojojin kasar, sun bayyana cewa mutane 31 suka rasa rayukansu sakamakon harin.

Tun dai bayan fara yakin, mayakan sun gina sansanoni a wuraren da mutane ke zaune kuma an zarge su da tilastawa 'yan kasar su bar muhallansu.

Babban sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Gutteres, ya yi Allah wadai da harin na ranar Lahadi wanda ya yi ikirarin "kamar yadda rahotanni suka nuna ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 22" tare da raunata da dama, kamar yadda mataimakin kakakin sa, Farhan Hak, ya bayyana.

Gutteres, "Ya damu matuka da cigaba da rikici a tsakanin sojojin wanda ya tura Sudan gaf da fadawa yakin basasa da zai iya shafar zaman lafiyar yankin." Kamar yadda Hak ya bayyana.

"Akwai rashin mutunta dokokin agaji da na bil-adama mai hatsari." Kamar yadda ya yi gargadi.

Kamar yadda kungiyar da ke kula da tafiye-tafiyen jama'a ta kasa-da-kasa ta bayyana, kusan mutane miliyan uku sun bar muhallansu sakamakon rikicin na Sudan, inda kusan 700,000 suka gudu zuwa kasashe makwafta.

Majalisar dinkin duniya da ta Afirka sun yi gargadin "bangaren kabilanci" ga rikicin da ake yi a yammacin yankin Darfur, inda mayakan RSF da sauran wadanda ke dauke da makamai ke da alhakin mafi yawan keta ka'idoji.

Hak ya goyi bayan Majalisar kasashen Afirka da majalisar kasashen gabashin Afirka ta IGAD a yunkurinsu na kawo karshen wannan al'amari na kasar Sudan.

Shugabanni daga kasashen Habasha, Kenya, Somaliya, Sudan ta Kudu - mambobin IGAD da ke kula da al'amurran na Sudan- za su hadu a ranar Litinin a Addis Ababa. 

Shugaban sojoji, Abdul Fattah al-Burhan, da kwamandan mayakan RSF, Mohamed Hamdan Daglo, duka an gayyacesu, kodayake ba wanda ya tabbatar da zuwan. 

A cikin yakin, an bayyana yarjeniyoyin tsagaita wuta wadanda daga bisani aka yi watsi da su.

No comments

Powered by Blogger.