Siriya ta harbo makamai masu linzamin Isra'ila kusa da birnin Homs
Makamai masu linzami a sama yayin da Isra'ila ta kai hari kan na'urar tsaron sararin samaniya da wasu wuraren sojoji a Damascus cikin shekarar 2018.
Na'urorin kula da sararin samaniyar kasar Siriya sun tarbe tare da harbo makamai masu linzami mallakin Isra'ila bayan da Isra'ilan ta kaddamar da sabbin hare-hare ta sama a kan wasu wurare a kusa da birnin Homs.
Kamar yadda kafar watsa labarai ta musamman a kasar Siriya, SANA, ta bayyana, an yi hare-haren ne a ranar Lahadi.
Sojojin Isra'ila sun yi harin "ne daga bangaren arewa-maso-gabashin (babban birnin kasar Lebanon) Beirut da niyyar samun wasu wurare kusa da birnin Homs." Kamar yadda wata majiyar sojoji ta bayyana.
Bayan hare-haren, na'urorin tsaron sararin samaniyar Siriya sun mayar da martani ta hanyar tarbe makamai masu linzamin Isra'ilan da ake harbowa inda suka kabe da dama.
Hare-haren sun haifar da asarar wasu kadarori ne kawai, kamar yadda majiyar ta bayyana.
Kakakin hukumar sojojin Isra'ila ya yi ikirarin cewa jiragen saman kasar sun yi niyyar samun wani wuri da ke dauke da na'urar tsaron sararin samaniyar Siriya ne inda daga nan ne aka harba wani makami mai linzami na harbo jirgin sama zuwa yankunan da aka mamaye, inda ba wanda ya raunata, kamar yadda kafar watsa labarai ta Press TV ta ruwaito.
Sabon harin na zuwa ne bayan harin makami mai linzami na tsakiyar watan Yuni wanda kasar ta yi a kan babban birnin Siriya wato Damascus.
Wannan harin kuwa ya zo ne daga yankin da Isra'ila ta mamaye na Golan Heights inda sojan Siriya daya ya samu raunuka tare kuma da haifar da asarar kadarori.
Isra'ila akai-akai ta na kai hare-hare a wuraren da sojojin Siriya suke da na kawayenta tun cikin shekarar 2011, lokacin da kasar ta Larabawa ta samu kan ta karkashin rikici da ta'addancin da ke samun goyon baya daga waje.
Kasar mafi yawanci ta na kai hare-hare ne a wuraren da sojoji kawayen Siriya suke wadanda ke taimaka mata a kan yakin da ta ke yi da 'yan ta'adda.
Damascus akai-akai ta shigar da korafi ga majalisar dinkin duniya kan hare-haren na Isra'ila, inda ta nemi kwamitin tsaro na majalisar da ya dauki mataki a kan laifuffukan na Isra'ila, sai dai bukatun na ta ba a saurari su ba.
Post a Comment