Header Ads

Yadda Shaikh Zakzaky ya yi radin sunan jikarsa a Abuja

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H), jikarsa Fatimah Naseemah da mahaifinta, Sayyed Mohammad Ibraheem, a wurin bukin radin sunan a ranar Lahadi a Abuja.

Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya jagoranci bukin radin sunan jikarsa, Fatimah Naseemah, a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli na shekarar 2023, wadda ta yi daidai da 20 ga watan Dhul al-Hijja, shekara ta 1444 bayan Hijira, a gidansa da ke Abuja.

Fatimah Naseemah, an haife ta ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Dhul al-Hijja, shekara ta 1444 wadda ta yi daidai da 2 ga watan Yuli na shekarar 2023. ita ce jika ta biyu ga Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) wadda dan sa na fari Sayyed Mohammad Ibraheem da matarsa, Malama Maimuna, suka haifa, yayin da jikansa na farko shine mai suna Nadeer, da na farko a wajen Sayyed Mohammad Ibraheem. 

Muna rokon Allah Ta'ala Ya albarkace ta, Ya sanya ta cikin salihan bayinSa alfarmar Annabi (S) da Ahlulbaiti (AS).

No comments

Powered by Blogger.