Header Ads

Rundunar sojojin ruwa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kama tanka dauke da tan 900 na mai da aka yi fasa kwaurin sa

Wasu sojojin ruwa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Rundunar sojojin ruwan Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRGC) ta kama tanka dauke daruruwan litocin mai wanda aka yi fasa kwaurinsa a tekun Fasha.

Kafar watsa labarai ta Fars news agency ta ruwaito a ranar Alhamis cewa sojojin na IRGC sun kama tanka dauke da mai wanda ke da nauyin tan 900 da aka yi fasa kwaurin sa, kuma sun kama duka mutane 12 da ke cikin tankar.

Ba a bayar da wani bayani na gaba ba dangane da tankar kuma an bayyana kasar da mutanen da ciki suka fito.

Bayan jaddada cewa kama tankar an yi ne a karkashin umarnin kotu, rahoton ya bayyana cewa sojojin ruwan na IRGC sun kama litocin mai da aka yi fasa kwaurin su sama da lita miliyan 50, mafi yawanci man dizil a ayyuka daban-daban da suka yi a shekarar da ta gabata.

Rahoton na zuwa ne a yayin da hukumar sufurin ruwa ta Iran ta bayyana cewa tana yunkurin ta kama wata tanka mallakin kamfanin makashin Amurka na Chevron da ya lalata wani jirgin ruwa na Iran a ranar 5 ga watan Yuli inda daga bisani ba kan ka'ida ba ya juya ya shiga cikin ruwan kasar Oman.

Mutane biyar suka samu mummunan rauni sakamakon karon a tsakanin tankar mai dauke da tutar Bahamas da kuma jirgin na Iran wanda ke dauke da mutane bakwai, kamar yadda kafar watsa labarai ta Press TV ta ruwaito.

Rundunar sojojin ruwan ta Iran, IRGC, a shekarun baya ta hana hare-hare da dama a kan tankokin Iran da kuma na sauran wasu kasashen a ruwan mai muhimmanci na tekun Fasha da ke yankin da kuma wasu manyan tekuna.

A cikin wani rahoto na kafar watsa labarai ta Fars news agency a cikin watan Afirilu, rahoton ya bayyana cewa kasar Iran na rasa dalar Amurka biliyan 4 a kowacce shekara sakamakon fasa kwaurin mai.

Alkaluma a cikin rahoton sun nuna cewa lita miliyan biyar ta man gasolin da ake rarrabawa masu motoci a Iran na karewa ne a hannun masu fasa kwauri da ke yin ayyukansu a kudu-maso-gabashi da iyakokin kudancin kasar.

Alkaluman sun nuna cewa wasu litoci miliyan 10 na man dizil su ma ana yin fasa kwaurin su a fitar da su daga Iran sakamakon raguwar kulawa a wasu wuraren makamashin Iran da ke kona dizil domin samar da wutar lantarki.

No comments

Powered by Blogger.