Header Ads

Kwarewar masu tiyata a Saudiyya wajen raba yaran da aka haifa a hade ta haskaka masarautar a duniya

Dakta Abdullah Al-Rabeeah tare da yara 'yan biyu da aka haifa a hade wadanda ya yiwa tiyata daga kasashe daban-daban a shekarar 2010.

A cikin shekaru sama da 30 na yin aiki cikin kwarewa na likitocin Saudi Arabiya masu yin tiyata a shirin raba yaran da ake haifa a hade ya sa yaran su kasance cikin koshin lafiya da yin rayuwa mai kyau kamar kowa, wannan ya sa masarautar ta zama shugaba wajen yin tiyata mai sarkakiya a cikin tarihin likitanci na wannan zamanin. 

A cikin wani rahoto na kafar watsa labarai ta Arab News, kafar ta bayyana babban likita mai tiyata, Dakta Abdullah Al-Rabeeah, a matsayin daya daga cikin wadannan likitoci. Likitan ya yi aiki a masarautar a matakai da dama da suka hada da ministan lafiya na masarautar, mai bayar da shawara ga kotun masarautar kuma babban mai kula da ayyukan cibiyar samar da agaji ta King Salman Humanitarian Aid and Relief Center, KSrelief.

A ranar Alhamis, Al-Rabeeah, cikin nasara ya raba wasu yara biyu da aka haifa a hade 'yan kasar Siriya, Basam da Ihsan, wadda aka kwashe awowi bakwai da rabi ana yi a kashi-kashi har kashi biyar, kuma tawagar likitoci kwararru 'yan kasar Saudiyya 26 suka yi wannan tiyata, kamar yadda kafar watsa labarai ta SPA ta ruwaito.

A tsawon shekarun da ya dauka yana aiki a matsayin likita mai yin tiyata, Al-Rabeeah ya yi tiyata kan yaran da aka haifa a hade har 58 daga iyalai marasa hali wadanda suka fito daga kasahe 23. Baki daya, shirin ya yi duba cikin irin wannan al'amari har sau 130, inda suka gudanar da daruruwan tiyata cikin awowi masu yawa.

Basam da Ihsan, wadanda an kawo su ne daga Turkiyya a cikin watan Mayu, kuma da ya ke sun kusa yin bukin ranar haihuwarsu, sai suke jin kunya. Basam da Ihsan suna a hade ne a bangaren kirji, ciki, hanta da hanji, baki daya nauyin su shine kilo 19. Duk da cewa Bassam yana cikin koshin lafiya, Ihsan ba a tunanin zai iya rayuwa fiye da 'yan kwanaki. 

"(Ana ganin Ihsan) a matsayin mai kutse a jikin Bassam saboda rashin mafitsara da abubuwan da suka danganci haihuwa a koda, jijiyoyin mafitsara, mafitsara da abubuwan da suka shafi haihuwa na namiji." Cewar Al-Rabeeah yayin bibiyar tiyatar, kamar yadda kafar watsa labarai ta SPA ta bayyana.

"Yana ma fuskantar matsala da ya samu daga haihuwa a zuciyarsa wadda ta shafi rayuwarsa da cigaban kwakwalwa, kuma yana fama da matsaloli a hanji."

Domin ceto rayuwar Bassam, tawagar ta likitoci sai ta yanke shawarar yin tiyatar mai sarkakiya domin raba 'yan biyun, "Wannan tiyatar aikin ceto ne ga Bassam , wanda shi ya ke cikin koshin lafiya." Kamar yadda tawagar likitocin ta shaidawa SPA.

Tiyatar da ake yi a shirin raba 'yan biyu da aka haifa a hade dai gwamnatin Saudiyya ce ke daukar nauyin ta. Wannan na sa yara su yi rayuwa mai tsawo cikin koshin lafiya, ba tare da kula da duk wani motsinsu ba kuma ba tare da matsalar kwakwalwa ko ta fili ba.

'Yan biyu da ake haihuwa a hade, wadanda akan kira da "Siamese twins" ba a cika samun su yayin haihuwa ba, inda ake samun su sau daya a duk haihuwa 50,000 zuwa 60,000. Wata kididdigar ta bayyana cewa ana samu ne sau daya a duk haihuwa 200,000 da aka yi.

Kamar yadda ilimin likitanci ya nuna, kusan kashi 60 na 'yan biyu da ake haihuwa a hade bari ake yi, yayin da kashi 40 ke rayuwa bayan haihuwa su rasu bayan 'yan kwanaki. Kusan kashi 70 na 'yan biyu da ake haihuwa a hade mata ne.

No comments

Powered by Blogger.