Kona Alkur'ani: Mun yi Allah wadai da wannan al'amari na abin kunya - The Assyrian Church of the East
Cocin Assyria da ke Gabas (The Assyrian Church of the East) ta yi Allah wadai da kona Alkur'ani mai tsarki da aka yi a babban birnin kasar Sweden, Stockholm, inda ta bayyana al'amarin da abin kunya.
Shugabancin Cocin Assyria da ke Gabas, a cikin wani jawabi wanda kamfanin dillancin labarun Iraki (INA) ya samu, ta bayyana cewa, "Kafofin watsa labaru sun bayyana cewa wani wanda ba shi da addini, dan asalin kasar Iraki, ya kona Alkur'ani, a ranar Laraba, 28 ga watan Yuni na shekarar 2023 a babban birnin kasar Sweden, Stockholm. Wannan aikin wani mutum ne shi kadai kuma ba ya nuni da matsayar Kiristanci baki daya, ba matsayar kuma kowacce Cocin Kirista ba."
Jawabin ya kara da cewa, "Dan haka shugabancin Cocin Assyria da ke Gabas a Iraki da kuma duniya baki daya ya yi Allah wadai da wannan al'amari na abin kunya da kakkausar murya, domin kaucewa wani abu ne da kowanne mutum ya kamata ya yi na girmama mutunci da imanin wasu.
"Aiwatar da cin mutunci a kan kowanne abu na wani addini abu ne wanda bai kamata ba da ke da niyyar haifar da kalaman batanci, a wani lokaci da ake bukatar mu da mu kasance masu samar da gada wadda za ta hada mu, mu samar da dangantaka ta so, iya zama da juna da girmamawa, saboda wannan shi zai sa mu samar da gada wadda za ta hada mu, ko da menene imanin mutum.'
Jawabin shugabancin cocin ya kara da cewa, "Cocin Assyria da ke Gabas, wadda aka kafa a karkashin koyarwar Kiristi da Baibul, a yau ta yi watsi, kamar yadda a kodayaushe ta ke yin watsi, da duk wasu matakai da ayyuka da ke da niyyar cutarwa ga abinda ya ke mai tsarki, wuraren bauta da kuma wadanda suka yi imani da wasu addinai, ta kowacce hanya, a kowanne lokaci, ta kowanne launi daga duk wani bangare ko wasu mutane."
Shugabancin cocin ya yi kira ga dukkan shugabannin addinai da "su gargadi mabiyansu da ka da su aikata wani abu na tsatstsauran ra'ayi da kuma rashin iya zama da wadanda ba daya kuke ba cikin mutunci" sai kuma ya yi kira ga duka shugabannin kasashe, musamman gwamnatin Sweden, da "ka da ta kyale irin wannan al'amari da ake yi da sunan 'yanci" sai aka kammala jawabin da cewa, "Duk wani 'yanci ya na da iyaka, mafi muhimmanci shi ne girmama mutunci da abubuwa masu tsarki na wasu. Wannan shi ne Baibul ya koya mana:"Ku kasance masu mutunta juna." (Ephesians 4:32), Kamar yadda kafar watsa labarai ta 7eNEWS ta ruwaito.
Post a Comment