Kashi 40 na yarukan duniya na fuskantar barazanar bacewa - UNESCO
Hukumar kula da ilimi da al'adu ta Majalisar dinkin duniya (UNESCO) ta bayyana cewa akalla kashi 40 cikin 100 na yarukan da ake magana da su a duniya na fuskantar barazanar bacewa.
Hukumar ta UNESCO ta bayyana cewa sama da yaruka 6,700 ake amfani da su a fadin duniya, sai dai kashi 40 suna fuskantar barazanar a manta da su, kamar yadda kafar watsa labarai ta Shia Waves ta ruwaito.
A ranar Litinin, 3 ga watan Yuli na shekarar 2023, hukumar ta tura wani sako inda a cikinsa ta bayyana cewa dakunan daukar darussa na taka muhimmiyar rawa wajen cigaba da rayar da yare.
Hukumar ta kasa-da-kasa ta nemi kasashe da su tabbatar da amfani da yaren mahaifiya wajen koyar da ilimi.
Post a Comment