Header Ads

Kananan yaran Falasdinawa na fama da cin zarafi mai yawa a kurkukun Isra'ila - Save the Children


Kananan yaran Falasdinawa na fama da cin zarafi a yanayin rayuwa da kuma a fili mai yawa a kurkukun Isra'ila, kamar yadda kungiyar Save the Children ta bayyana a cikin wani sabon rahoton ta wanda aka wallafa a ranar Litinin.

Akwai hauhawar yawan matasan Falasdinawa da ke fama da tsoro da rashin iya yin barci da kuma rashin cigaba da rayuwarsu yadda suka saba saboda halin da suka samu kan su a ciki a kurkuku, kamar yadda kungiyar ta kare hakkokin bil-adama ta bayyana.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Press TV ta ruwaito, wasu daga cikin yaran sun yi magana dangane da cin zarafi mai kama da keta haddi. Da yawa an duke su, an daure masu hannuwa, an rufe masu idanu a cikin kananan keji a wuraren tsare mutane, kuma akan kaisu wasu wuraren da ake tsare mutane, kamar yadda Save the Children ta bayyana. Ana ma yi masu tambayoyi a wuraren da ba su san ko ina ba ne, ba kuma tare da mai kula ba, sannan akan hana su abinci, ruwa da barci.

Gwamnatin ta Isra'ila kan ma hana kananan yaran na Falasdinawa samun damar samun lauyan doka.

Rahoton ya bayyana cewa kashi 86 na kananan yara 228 da aka kulle wadanda aka yi bincike kan su an duke su yayin da suke a kulle, kashi 69 an tube su ko wani bangaren su domin bincikensu. Kashi 42 an raunata su lokacin da aka kama su; raunukan sun hada da raunuka daga harbin bindiga da kuma karyewar kashi.

Khalil, wanda aka kama lokacin yana da shekaru 13, ya ce bai samu wata kulawar likitoci ba.

"Ina da rauni a kafa ta. An daure wurin kuma dole in ja jiki domin in iya matsawa. Ina ji kamar jikina zai tsage. Ba ni da sandar da zan dogara domin ta taimakamin wajen iya tafiya, na cigaba da neman sojojin da su taimaka min yayin da aka kai wajen amma ba wanda ya taimake ni." Kamar yadda Save the Children ta bayyana yadda ya ke cewa.

Kungiyar ta ce yaran da aka bincika wadanda aka taba kullewa a kurkuku sun fito ne daga yankin Gabar yamma da kogin Jordan da aka mamaye kuma an kulle su ne a tsakanin wata daya zuwa watanni 18.

"Babban laifin wannan kullewar shine jifa da dutse, wanda na iya sawa a yanke hukuncin zama kurkuku har na tsawon shekaru 20 ga yaran Falasdinawa." Kamar yadda Save the Children ta ruwaito.

Jason Lee, daraktan Save the Children a yankin Falasdinawa da aka mamaye, ya bayyana cewa yaran Falasdinawa su ne kawai kananan yara 'yan kurkuku da ake yankewa hukunci a kotunan soja a duniya.

"Binciken mu - ya sake nunawa - cewa (yaran Falasdinawa) na fuskantar cin zarafi babba wanda ya fadada a hannun wadanda ya kamata a ce suna kulawa da su." Kamar yadda Lee ya bayyana.

Save the Children ta bayyana cewa irin wadannan al'amurra sun dade suna damun hakkokin bil-adama.

No comments

Powered by Blogger.