Header Ads

Fafaroma Francis ya yi Allah wadai da kona Alkur'ani a kasar Sweden

Shugaban Cocin Katolika, Fafaroma Francis

Shugaban Cocin Katolika, Fafaroma Francis ya bayyana cewa ya yi watsi da amincewa da a kona Alkur'ani da aka yi a cikin wata tattaunawa da ya yi da wata jaridar kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta al-Ittihad a ranar Litinin, inda ya kara da cewa wannan al'amari ya bata masa rai, kamar yadda kafar watsa labarai ta Arab News ta bayyana. 

"Duk wani littafi da aka dauke shi mai tsarki, ya kamata a girmamam shi domin girmama wadanda suka yi imani da shi." Kamar yadda Fafaroman ya bayyana, "Na ji haushi da kyamar wannan al'amari." 

Kalaman sune irinsu na farko da wani shugaban Cocin Katolika ya yi dangane da kona kwafin Alkur'ani a kasar Sweden.

"Kyale hakan abin Allah wadai ne kuma wanda ba za a amincemawa ba." A cewarsa, inda ya bayyana cewa hakkin fadin albarkacin baki bai kamata a yi amfani da shi a matsayin dalilin bata ran wasu ba.

"Yunkurinmu shine a mayar da hankali wajen addini ta hanyar hadin kai, 'yan uwantaka da yin ayyuka masu kyau na taimakon juna." 

Wani mutum ne dai mai suna Salwan Momika, ya yaga tare da kona Alkur'ani a babban birnin kasar Sweden a cikin satin da ya gabata, wanda hakan ya jawo yin Allah wadai daga kasashe da dama.

A yayin da 'yan sandan Sweden sau da dama sun sha hana yunkurin gudanar da zanga-zangar kona Alkur'ani a kasar, wata kotu ce ta dakatar da matakin na su, inda ta bayyana cewa hakan ya keta hakkin fadar albarkacin baki.

A ranar Lahadi, Kungiyar Kasashen Musulmi mai dauke da kasashe 57 ta bayyana cewa ana bukatar daukar mataki na bai daya wanda zai hana keta alfarmar Alkur'ani kuma ya kamata a yi amfani da dokar kasa-da-kasa domin hana kiyayyar addini.

No comments

Powered by Blogger.