Header Ads

Dalilin da ya sa muka dakatar da albashin ma'aikata 10,800 - Gwamnatin jihar Kano

Gwmnan jihar Kano, Abba Yusuf Kabir

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ma'aikatan jihar da aka dakatar a 'yan kwanakin nan ba a kore su daga aiki ba tukunna.

Ma'aikatan guda 10,800 gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Ganduje, ce ta dauke su aiki.

An bayyana haka ne a ranar Juma'a a yayin wani taron hadin gwiwa tsakanin kwamishinan watsa labarai, Malam Baba Dantiye; Akanta Janar, Abdukadir Abdulsalam da shugaban ma'aikata (HOS), Usman Bala-Muhammad.

Shugaban ma'aikatan ya bayyana cewa ma'aikatan guda 10,800 ba an kore su daga aiki ba ne, amma an tsayar da albashin su ne kafin a tantance matsayinsu.

"'Bari in fayyace komai, ba wani ma'aikacin da aka kora, amma dai an tsayar da albashinsu kafin a tantance matsayinsu.

"Za a samar da kwamitin tantancewa nan ba da jimawa ba kuma bayan an kammala aikin, wadanda aka dauka a kan ka'ida kamar yadda dokar ma'aikata ta tanadar, za su karbi albashin su.'

Kamar yadda ya bayyana, amfanin shine inganta bangaren ma'aikata domin su yi aiki yadda ya kamata kuma su sa komai a inda ya dace.

Gwamnatin ta bayyana jin dadin ta da yadda ma'aikata da 'yan fansho a jihar su ka yi hakuri da kuma murnar da suka nuna bayan sun karbi albashinsu na watan Yuni ba tare da an cire komai ba, kamar yadda kafar watsa labarai ta PM News ta ruwaito. 

Akanta Janar din yayin da ya ke amsa tambayoyi, ya bayyana cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ne ya bayar da umarni ga ofishinsa da ya dakatar da albashin ma'aikatan 10,800 wadanda Ganduje ya dauka aiki.

Abdulsalam ya ce za a kafa kwamiti wanda zai duba ka'idojin da aka bi wajen daukar su aiki saboda wadanda aka dauka ba bisa ka'ida ba a cire su.

Kamar yadda ya bayyana, gwamnatin da ta wuce ta dauki ma'aikata da kuma kara masu matsayi ne kawai lokacin da mulkin ta ya zo karshe.

Dangane da ma'aikatan kananan hukumomi, Abdulsalam ya bayyana cewa wadanda gwamnatin da ta gabata ta mayar da su ma'aikatan jiha za su cigaba da karbar albashinsu.

Abdulsalam ya bayyana cewa abinda gwamnatin mai ci ta yi zuwa yanzu yunkuri ne na gyara tsarin domin samar da aiki ingantacce.

No comments

Powered by Blogger.