Header Ads

Ƙasar Sweden ba za ta shiga NATO ba bayan tana ruruta kiyayya da Musulunci - Erdogan

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana rashin amincewar Ankara na yarda da shigar kasar Sweden cikin hadakar tsaro ta Kungiyar NATO da Amurka ke jagoranta tare kuma da Allah wadai da Stockholm kan tunzura abubuwan da za su haifar da nuna kiyayya da Musulunci da kuma samar da mafaka ga 'yan ta'adda a kasar ta.

Erdogan ya kara da kokawa kan keta alfarmar Alkur'ani mai tsarki da aka yi a babban birnin kasar Sweden, inda ya bayyana harin da "aikin matsorata" a kan Musulunci "da ya bata ran mu baki daya" a cikin wani jawabi da ya yi bayan wani taro da majalisa a Ankara.

"Wannan laifi ne na kiyayya da ke ruruta kiyayya da Musulunci" kamar yadda ya bayyana, inda ya jaddada cewa hari kan wani abu da mutane ke dauka mai tsarki ba za a bayyana shi da 'yancin fadar albarkacin baki ba.

"Kamar kona majami'a, wurin bautar Yahudawa ko ginin bauta na wani imani ba 'yancin fadar albarkacin baki bane, saboda haka babu wani 'yanci na kona Alkur'ani." Kamar yadda shugaban na Turkiyya ya bayyana. 

Erdogan ya yi magana kan gazawar kasashen yamma wajen kawo karshen ayyukan nuna kiyayya da Musulunci.

Shugaban na Turkiyya ya ma nuna bacin ransa kan Sweden sakamakon cigaba da samar da mafaka ga Kurdawa wadanda Ankara ke kallo da 'yan ta'adda masu neman warewa.

"Mun bayyana karara cewa dagewa kan fada da kungiyoyin 'yan ta'adda da nuna kiyayya da Musulunci shine jan layin mu." Ya jaddada.

"Kowa ya kamata ya amince cewa ba za a samu abokantakar Turkiyya ba ta hanyar taimakon ta'addanci ko kuma samar da mafaka ga 'yan ta'adda." Kamar yadda ya kara da cewa.

Domin dai shiga kungiyar NATO, kasar Sweden na neman amincewar baki daya mambobin kungiyar na yanzu, ciki har da Turkiyya, wadda ta ke a kungiyar ta hadaka tsawon shekaru 70 kuma ita ke da sojoji wadanda suka fi yawa na biyu a cikin kungiyar.

Duk da cewa shugabannin NATO suna fatar shigar Sweden cikin kungiyar kafin wani babban taro da za a yi zuwa karshen wannan watan a Lithuania, kasashen Turkiyya da Hungary sun ki amincewa.

No comments

Powered by Blogger.