Header Ads

Argentina, Brazil da Mexico sun yi Allah wadai da cin zarafin da Isra'ila ta yi a Jenin inda mutane 12 suka rasu, 140 suka raunata

Wani Bafalasdine da sojojin Isra'ila suka raunata a ranar 4 ga watan Yuli na shekarar 2023.

Gwamnatocin Argentina, Brazil da Mexico sun yi kira da a kawo karshen rikicin da ke faruwa a Falasdinu tare da kira ga bangarorin da abin ya shafa su kaucewa ruruwar al'amarin.

"Gwamnatocin Argentina, Brazil da Mexico sun samu labari mai tayar da hankali cewa Isra'ila ta kaddamar da wani babban kutse na soji a birnin Jenin na Falasdinu a Gabar yamma da kogin Jordan ... Suna yin ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu suna kuma neman duka bangarorin da abin ya shafa su kawo karshen rikicin domin hana yaduwarsa da haifar da karuwar yawan fararen hula da suka raunata, tayar da mutane daga muhallansu da kuma lalata gine-ginen da ke birnin Jenin." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin hadaka wanda Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen Mexico ta rarraba a ranar Talata.

Gwamnatin Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama da ta kasa mafi girma a cikin shekaru a ranar Litinin, inda rundunar sojojin saman Isra'ila (IDF) ta kai hare-hare ta sama fiye da 10 a abinda ta kira "gine-ginen 'yan ta'adda" a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin.

Kasashen uku na nahiyar Amurka ta Kudu sun yi Allah wadai da ta'addanci kowanne iri tare da kira da a girmama dokokin kasa-da-kasa na agaji tare da kiran a samar da mafita ta kasa-biyu inda Falasdinu da Isra'ila za su wanzu a karkashin kan iyakoki da kasashen duniya suka amince da su.

Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu a ranar Talata ta bayyana cewa mutane 12, ciki har da yara biyar, aka kashe yayin da mutane 140 suka raunata yayin kutsen da Isra'ila ta yi, inda fararen hula 30 suke cikin mawuyacin hali.

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, a ranar Talata ya bayyana cewa Isra'ila ta kawo karshen hare-haren da ta ke yi a birnin Jenin da ke Gabar yamma da kogin Jordan.

A ranar Litinin ne dai Isra'ilan ta kaddamar da wasu manyan hare-haren ta sama da ta kasa a Jenin da sansanin 'yan gudun hijira da ke wurin, inda ta kashe akalla Falasdinawa goma tare da raunata da dama, wasu daga ciki an bayyana cewa suna cikin mummunan yanayi. Harin ya cigaba zuwa ranar Talata kamar yadda kafar watsa labarai ta Press TV ta ruwaito.

Wannan harin sojin ana kallonsa a matsayin wanda ya fi girma a Gabar yamma da kogin Jordan a cikin shekaru inda kasar ta Isra'ila ta girke jirage marasa matuka dauke da makamai da kuma daruruwan sojoji a kan Falasdinawa marasa laifi.

Sojojin na Isra'ila sun ma tursasawa daruruwan Falasdinawa barin muhallansu domin shirin rushe su saboda kaiwa ga mayakan da ke fafutika.

Wannan matakin na Isra'ila ya haifar da yin Allah wadai daga kasashen Musulmi da wadanda ba na Musulmi ba.

No comments

Powered by Blogger.