Header Ads

An sanya dokar taƙaita zirga-zirga a jihar Adamawa


s

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya ayyana dokar ta-ɓaci ta tsawon sa'a 24 a fadin jihar.

Cikin wani saƙon da gwamnan ya wallafa a shafinsa ta twitter, ya ce an sanya dokar ne sakamakon ƙaruwar hare-haren da ɓata-gari ke kai wa mutane da kasuwanni a faɗin jihar.

Rahotonni daga jihar sun ce wasu ɓata-gari ne suka riƙa far wa mutane da makamai a birnin Yola tare da sace musu dukiyoyi a shagunansu.

Gwamna Fintiri ya ce an hana zirga-zirga a jihar, sai iya mutanen da ke ayyuka na musamman, waɗanda ke ɗauke da katin shaidar aiki.

Gwamnan wanda ya yi kira ga al'ummar jihar da su yi biyayya ga dokar, ya ce tsaron lafiyar mutanen jihar shi ne babban abin da ya sanya a gaba.


No comments

Powered by Blogger.