An kawata haramin Imam Ali da ke Najaf domin ranar Eid al-Ghadeer
An kawata haramin Imam Ali da ke Al-Najaf Al-Ashraf da tutoci na musamman da alluna domin shirye-shiryen bukukuwan Eid al-Ghadeer a ranar Juma'a, 18 ga wata mai tsarki na Dhul Hijja.
Tutocin da allunan, wadanda aka sanya su a duka bangon haramin mai tsarki, suna dauke ne da bayanai wadanda ke nuni da yin biyayya ga Imam Ali bin Abi Talib (AS). Kawata haramin na cikin bangaren ayyukan da ake yi daban-daban cikin ranaku goma na bukukuwan na Ghadeer, kamar yadda Shia Waves ta ruwaito.
'Yan Shi'a dai a fadin duniya sukan gudanar da bukukuwan Ghadeer ko Eid al-Ghadeer a kowacce shekara. Yana daya daga cikin muhimman bukukuwa da 'yan Shi'a ke yi a ranar 18 ga watan Dhul Hijja da ke cikin kalandar Hijira.
Ita ce ranar da Manzon Allah (S) ya nada Imam Ali Ibn Abi Talib (AS) a matsayin kalifansa kuma shugaba a bayansa da umarni daga Allah.
Babban malamin addini, Ayatollah Sayyid Sadik al-Husseini al-Shirazi, ya bukaci musulmai baki daya da su gudanar da bukukuwan kwanaki goma na Ghadeer domin su sanar da duniya yin biyayyar ranar Ghadeer da kuma muhimmin tarihin Imam Ali (AS).
Post a Comment