Header Ads

Almajiran Sheikh Zakzaky sun yi muzahara a babban masallacin kasa da ke Abuja domin yin Allah wadai da kona Alkur'ani a Sweden

'Yan uwa musulmi almajiran shugaban harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, sun yi muzahara a babban masallacin kasa da ke Abuja (Central Mosque) domin yin Allah wadai da kona Alkur'ani mai tsarki a kasar Sweden.

Almajiran na Sheikh Zakzaky sun fara muzaharar ne tun daga cikin masallacin inda suka hau sahu, inda kuma suke tafe suna rera wakokin kin amincewarsu da cin mutuncin da kasar Sweden ta yi wa Alkur'ani, tare da tsinewa kasar da magoya bayan ta'addancin da aka yi na kona Alkur'ani.

Masu muzaharar, wadanda suka nuna goyon bayansu ga Alkur'ani, daga karshen muzaharar sun kona tutar kasar Sweden tare da daga Alkur'ani. 

A dai ranar Laraba ne, ranar da ake gudanar da Eid Al-Adha bayan kammala aikin Hajji a Makkah da ke Saudi Arabiya, wani mutum mai suna Salwan Momika mai shekaru 37 ya taka Alkur'ani sannan ya sawa shafukansa da dama wuta a kusa da babban masallacin da ke Stockholm. Wannan cin mutunci ga littafi mai tsarki na Musulmai an yi shi ne karkashin yarda da kariyar 'yan sandan Sweden.

Wannan mummunan al'amari ya bakanta ran Musulmai a fadin duniya. 

A ranar Juma'a, dubban 'yan kasar Iraki sun taru a rana ta biyu a Jere domin nuna rashin amincewarsu da al'amarin.

Mutane a sauran kasashen musulmai su ma sun hau kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da al'amarin, kuma kasashe da dama sun yi Allah wadai da al'amarin wadanda suka hada da Saudi Arabiya, Iraki, Jordan, Kuwait, Iran, Moroko da Turkiyya.

A Nijeriya an gudanar da muzaharori a Kaduna, Kano, Bauchi, Potiskum da Abuja domin yin Allah wadai da kona Alkur'ani mai tsaki da aka yi a kasar ta Sweden.

No comments

Powered by Blogger.