Header Ads

Almajiran Sheikh Zakzaky sun kona tutar Sweden a Kano sakamakon kona Alkur'ani a kasar

Wakilin 'yan uwa a jihar Kano, Dakta Sunusi Abdulkadir yayin da ya ke jawabi.


Almajiran shugaban harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, da ke Kano sun yi Allah wadai da kona Alkur'ani da aka yi a kasar Sweden tare da kona tutar kasar. 
Al'amarin na zuwa ne bayan da wani mutum mai suna Salwan Momika a kasar Sweden ya kona Alkur'ani a ranar Idi, wanda hakan ya fusata musulmai a fadin duniya da ke cikin kasashe da dama.

Dakta Sunusi Abdulkadir, wanda ya ke shi ne wakilin 'yan uwa a jihar Kano, ya gabatar da jawabi dangane da al'amarin inda cikin batutuwan da ya kammala jawabinsa da su har da kira ga kasar nan da ta katse huldar jakadanci da Sweden kamar yadda wasu kasashen musulmi suka yi.

Bayan jawabin na sa, Dakta Suleiman Gambo ya yi takaitaccen jawabi da da harshen turanci daga bisani kuma aka taka tutar kasar Sweden tare da kona, sai kuma aka yi addu'ar Allah wadai da kasar ta Sweden. 

Kasashe da dama a fadin duniya sun yi Allah wadai da kona Alkur'ani da aka yi a kasar ta Sweden wadanda suka hada da Turkiyya, Saudi Arabiya, Iran, Kuwait, Moroko, Jordan, Iraki inda kuma musulmai suka gudanar da zanga-zanga a wasu kasashen musulmai da na turai ciki har da Sweden.

No comments

Powered by Blogger.