Header Ads

A Kaduna an yi muzaharar Allah wadai da kona Alkur'ani a Sweden

Wani sashe na masu muzaharar

A garin Kaduna, almajiran shugaban harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, sun gabatar da muzahara domin yin Allah wadai da kona Alkur'ani da aka yi a kasar Sweden.
Muzaharar wadda aka gabatar a ranar Talata, 4 ga watan Yuli, 2023, an fara ta ne da misalin karfe 5:00 na yamma daga mahada (junction) na Kano Road kan babban titin Ahmadu Bello Way da ke tsakiyar garin Kaduna inda kuma muzaharar ta kai har bakin Mangal Plaza inda a nan ne aka rufeta.

Masu muzaharar maza da mata wadanda sun fito ne domin nuna damuwarsu da kona Alkur'ani da aka yi a kasar ta Sweden da kuma shelanta rashin yardarsu ga wannan cin zarafi ga al'ummar musulmi, sun ja tutar kasar ta Sweden a kasa tare da fadin "Allahu Akbar ba mu yarda da kona Alkur'ani ba." 

Bayan kulle muzaharar, an yi kabbarori sannan aka kona tutar kasar ta Sweden sannan aka yi addu'o'i aka sallami mutane, kamar yadda Kaduna Struggle Media ta bayyana a cikin wani bayani kan muzaharar da ta yi.

A dai ranar Larabar da ta gabata ne wani dan kasar Iraki mai shekaru 37, ya taka Alkur'ani sannan ya sawa shafukansa da dama wuta a kusa da babban masallacin da ke Stockholm. Wannan cin mutunci ga littafi mai tsarki na Musulmai an yi shi ne karkashin yarda da kariyar 'yan sandan Sweden.

Wannan al'amari, wanda ya faru lokacin da ake gudanar da bukukuwan Eid Al-Adha bayan kammala aikin Hajji a Makkah da ke Saudi Arabiya, ya bakanta ran Musulmai a fadin duniya. 

Kasar Sweden akai-akai ta sha kyalewa a kona Alkur'ani a cikin shekarun nan. Ko a cikin watan Janairu, wani dan kasar Denmark a Sweden mai tsatstsauran ra'ayi ya kona Alkur'ani kusa da ofishin jakadancin Turkiyya da ke Stockholm.

No comments

Powered by Blogger.