Header Ads

Zelensky ya yi kira da a sa takunkumi ga Iran har na shekaru 50

Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky

Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya yi kira ga majalisar kasar da ta yarda da wani kuduri da ya shafi sa takunkumi na shekaru 50 kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran biyo bayan ikirarin da ake yi cewa Iran na da hannu wajen samar da makamai ga kasar Rasha.

Kudurin, wanda aka gabatar a ranar Lahadi, ya hada da hana safara baki daya da Iran, zuba jari da musayar fasaha.

Kudurin ya haramtawa Iran bi ta cikin kasar ta Ukraine da kuma bi ta sararin samaniyar ta tare da hana Iran kwashe kadarorinta daga kasar wadda ke arewacin nahiyar turai kamar yadda kafar watsa labaru ta Teghrib News Agency ta ruwaito.

Kudurin ya ma haramta babban bankin kasar Ukraine yin rijistar biyan kudade na kasa-da-kasa wanda Iran ke amfani da shi, wanda ke neman majalisar kasar, hukumar leken asiri a kasashe da kuma hukumar tsaro da su tattabar da kudurin takunkumin wanda ba zai yi wa Iran dadi ba.

Ana sa ran majalisar kasar Ukraine ta amince da kudurin wanda tuni ya samu amincewar majalisar tsaro ta kasar.

Kamar yadda shafin majalisar kasar ya nuna, ba su fitar da ranar da za su yi zabe a kan kudurin ba tukunna.

Shugaban ma'aikata na Zelensky, Andry Yermak, ya bayyana cewa kudurin martani ne ga ikirarin da ake yi na cewa Iran na samar da makamai ga Rasha.

A cikin wani jawabi da ya yi a wani bidiyo a satin da ya gabata Zelensky ya yi wannan ikirari a kan Iran, sai dai a matsayin martani, kakakin Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen Iran, Nasser Kan'ani ya bayyana cewa shugaban kasar ta Ukraine na "nuna siyasa" ne kawai cike da ikirarin "da bai da wani amfani" a kokarinsa na samun makamai masu yawa daga kasashen yamma.

"Maimaita ikirarin karya da shugaban kasar Ukraine ke yi a kan Jamhuriyar Musulunci yana kan layin farfaganda ne da yaki na kafafen watsa labaru na wadanda ba sa son Iran ga gwamnatin Iran da mutanenta da niyyar samun makamai masu yawa da taimakon kudade daga kasashen yamma." Kamar yadda ya bayyana a cikin wani jawabi a ranar Asabar.

Kasar Ukraine da kasashen yamma sun sha maimaita zargi kan Iran cewa tana samar jiragen yaki marasa matuka ga Rasha domin ta yi amfani da su a yaki, wani zargi wanda Iran ta yi watsi da shi kai tsaye.

No comments

Powered by Blogger.