Header Ads

Yara miliyan 20 da ba su zuwa makaranta a Nijeriya tushe ne na Boko Haram a nan gaba - Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Obasanjo 

Tsohon shuganan kasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi gargadin cewa yara miliyan 20 da ba su zuwa makaranta a Nijeriya tushe ne na Boko Haram a nan gaba. 

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne yayin wani taron kaddamar da littafi mai suna, 'Pillars of Statecraft: Nation-building in a changing world' wanda 'yar sa, Dakta Kofo Obasanjo-Blackshire, ta rubuta, a ranar Juma'a a jihar Legas.

Obasanjo ya bayyana cewa kasar a yanzu haka ta na da yara sama da miliyan 20 da ba su zuwa makaranta.

Ya kalubalanci 'yan Nijeriya da su duba a shafin bincike na google kasashe nawa ne suke da kasa da miliyan 20, inda ya yi tambaya: "Wannan bai dame mu ba? Muna tunanin ba za a samu Boko Haram ba gobe? 

"Wadannan sune tushen Boko Haram din ku gobe. Wannan ya kamata ya dame mu. Kada mu ce daga waje ne aka haifar.

"Shi ma talauci daga waje ne aka haifar? Talauci zabi ne a sane ko ba a sane ba na shugabanninmu. In mun ce a'a, to zai kasance a'a. In mun ce E, to zai kasance E." 

Kamar yadda kafar watsa labarai ta The Punch ta ruwaito, Obasanjo ya bayyana cewa yayin kwanakin farko na Boko Haram, lokacin da aka ce an kashe mutumin da ya fara ta, ya ce yana so ya hadu da mambobin kungiyar ya yi magana da su a ji me suke so.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa ya hadu da wakilan kungiyar tare da gano cewa babu abinda suke so sai rayuwa mai kyau, inda ya kara da cewa, "Shin za mu ga laifin su domin suna neman samun rayuwa mai kyau? 

"Sun ce sun yi imani da dokar Shari'a. Na fada masu Shari'a ba matsala ba ce a Nijeriya. Wani bangare ne na tsarin mulkin mu."

"Shin za mu ga laifinsu in bayan shekara hudu ba su da aiki? Shin ba suna da hakkin rayuwa mai kyau ba? Wannan ya shiga cikin daya daga cikin P's na gina kasa - politics (siyasa) - wanda ke magana a kan gwamnati da shugabanci.

"Idan har (shugabanci) ba a kula da shi ba sosai ba, duk kuma sauran wani abu zai sukurkuce. Dole mu tambaya, "Me za mu yi da mutanenmu? Ta yaya za mu daga su mu girmama su? Ta yaya za mu girmama su?." Kamar yadda Obasanjo ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.