Header Ads

'Yan ta'addan ISWAP da iyalansu 82 da suka gujewa fada da sojoji sun nutse a cikin kogi

Wasu 'yan ta'addan ISWAP

Akalla mayakan ISWAP 82 da iyalansu ne suka nutse a rafi a yankin arewa maso gabashin Damasak da ke jihar Borno, kamar yadda kafar watsa labaru ta PM News ta ruwaito.

An ruwaito cewa 'yan ta'addan da iyalansu daga yankin tafkin Chadi sun nutse ne a kokarinsu na gujewa kutsowar da rundunar sojoji suka yi a tsakanin ranakun 2 zuwa 3 ga watan Yunin shekarar 2023 yayin da suke kokarin tsallaka kan iyaka domin shiga kasar Nijer.

Majiyoyin tattara bayanan sirri sun bayyanawa Zagazola Makama, wani kwararre wajen yaki da masu dauke da bindiga kuma mai sharhi kan tsaro a tafkin Chadi cewa al'amurran da suka faru daban-daban an yi su ne a tsakanin Bulama Modori, Kaneram, Dogomolu da al'ummun Jokka.

Tsawon rafin ya fara ne daga Komadougou a Yobe zuwa tafkin Chadi zuwa Nijer.

Majiyoyin sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun yi yunkurin gudu ne bayan sun ji tsoron kashe su a filin yaki bayan sun ji labarin aikin da sojoji ke gabatarwa a yankin baki daya.

Mafiyawancin wadanda suka rasa rayukansu din mata ne da kananan yara wadanda ba su iya ruwa ba yayin da da dama kuma suna samun sauki.

An ruwaito cewa har yanzu ana gano gawarwaki.

No comments

Powered by Blogger.