Header Ads

'Yan bindiga sun sace wani babban limami a jihar Ondo

Babban limamin al'ummar USO, Ibrahim Bodunde-Oyinlade

'Yan sanda a jihar Ondo sun tabbatar da sace Ibrahim Bodunde-Oyinlade, babban limamin al'ummar USO da ke karamar hukumar Owo da ke jihar.

Malamin mai shekaru 67 an sace shi ne a gonarsa da ke Asolo Farm Camp da yammacin ranar Asabar.

Wani daga cikin iyalansa ya bayyana cewa sun kai rahoto wajen 'yan sanda lokacin da suka ga Malam Bodunde-Oyinlade bai dawo ba har wajen karfe 2:00 na dare, ba a daukar kira in an kira wayarsa, kamar yadda kafar watsa labarai ta PREMIUM TIMES ta ruwaito.

"Masu garkuwar sun yi magana da iyalan amma ba su kai ga maganar neman kudin fansa ba." Ya bayyana ba tare da barin an fadi sunansa ba.

Kakakin 'yan sandan jihar, Olufunmilayo Odunlami-Omisanya, ya tabbatar da faruwar al'amarin.

Ya bayyana cewa 'yan sanda da kuma 'yan bijilanti sun shiga cikin dajin domin neman limamin.

Mista Odunlami-Omisanya, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) cewa an samu mota da wayar limamin a gonar.

"Da kimanin karfe 6:00 na yamma ne iyalan suka zo suka yi rahoto ofishin 'yan sandan da ke USO.

"Shugaban 'yan sandan yankin (DPO), jami'an 'yan sanda da 'yan bijilanti na yin bincike a yankin domin kokarin yin ceto." Kamar yadda ya kara da bayyanawa.

No comments

Powered by Blogger.