Header Ads

Yadda wasu Kiristoci suka taimaka wajen share Filin Idi a jihar Kaduna

Wasu kirisysunntaiamaka wajen gyaran masallacin Idi

Wasu kiristoci a karamar hukumar Kachiya da ke kudancin jihar Kaduna sun taimakawa Musulmai wajen sare ciyawu a filin da ake amfani da shi wajen yin sallar Idi.

Shugaban tawagar kiristoci da suka hadu da musulmai wajen aikin, Daniel Bitrus, ya bayyana cewa sun yi hakan ne domin inganta dangantaka a tsakanin addinai.

A tare dai Musulman da Kiristocin suka sare ciyawun tare da cire duk wani abu da ba a bukata a wajen.

Bitrus ya bayyana cewa an kwashe kwanaki biyu ana yin aikin.

"Mun zo nan ne domin mu taimakawa 'yan uwanmu sare ciyawu da kawar da duk wani abu da ba a bukata a masallacin da kewayensa, da niyyar karfafa zaman lafiya da hadin kai.

"Aikin, wanda aka yi shi a cikin kwanaki biyu (Asabar da Lahadi), ya taimakawa Musulmai da Kiristoci wajen tattaunawa, karfafa abokantaka da yin magana a hanyoyin da suka dace domin karfafa iya zaman tare da kuma iya fahimtar juna da kyau a tsakanin mabiya addinan biyu.

"Muna fatar mu cigaba da yin haka a kowacce shekara domin mu karfafa iya zaman tare a tsakanin addinai a yankin." Kamar yadda ya bayyana a cikin wani rahoto na Daily Trust.

Yayin da ya ke jawabi dangane da al'amarin, Sakataren kungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI) reshen karamar hukumar Kachiya, Mallam Ibrahim Tasiu, ya bayyana jin dadinsa da yadda Musulman da Kiriatocin suka fita aikin sosai.

Ya kuma yabawa Kwamitin Tabbatar da Zaman Lafiya a Tsakanin Addinai (IMC), Hukumar Tabbatar da Zaman Lafiya a Jihar Kaduna (KAPECOM) da tawagar Mercy Corps kan rawar da suke takawa wajen bunkasa zaman lafiya kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

A nasa bangaren, Ko'idinetan kungiyar ta IMC a jihar Kaduna, Samso Auta, ya taya Musulmai murnar Sallah Babba, tare da yi masu fatan yin shagulgula lafiya.

No comments

Powered by Blogger.