Header Ads

Wanene Imam Khomeini?

Imam Khomeini 

Marigayi Ayatollah Ruhollah Mosavi Khomeini wanda aka fi sani da Imam Khomeini an haifeshi ne a ranar 24 ga watan Satumbar shekarar 1902. Mahaifinsa shine Agha Mustafa Mujtahid Kamareh'i. Ruhollah jika ne ga Seyyed Ahmad kuma jikan-jikan Deen Ali Shah. Ruhollah ya rasa mahaifinsa a lokacin da ya ke da watanni hudu a duniya.

Kamar yadda wani rahoton kafar watsa labaru ta Teghrib News Agency ya bayyana, bayan ya koyi Al-Qur'ani a garinsu, Ruhollah ya tafi makaranta lokacin da ya ke da shekaru bakwai. Ya fara daukar darussa daga Mullah Abul Qasim. Sai kuma ya tafi Maktabkaneh ta Sheikh Jafar. 

A farkon shekarun Imam Khomeini abubuwa da dama sun faru a Iran. A Khomein masu mulki wadanda ba su da adalci su ke da iko kuma kasar ba ta da tsaro. Rayuwa ta tsananta ga mutane, kuma lokacin da aka fara yakin duniya na biyu (World War II), abubuwa sai suka tsananta, cututtuka suka barke, talauci ya yadu kuma akwai fari mai tsanani.

Lokacin da Hajj Abdul Karim Ha'erri Yazdi ya shiga Arak ya kafa Makarantar Tauhidi, wadda nan-da-nan ta hadu da Makarantar Tauhidi da ke Isfahan kuma wadda a lokacin itace ta fi kowacce a kasar. Saboda haka, sai Ruhollah ya yanke shawarar shiga wannan sabuwar Makarantar Tauhidi ya kuma tafi Arak, wadda ke da nisan kilomita 60 daga Khomein. A nan, Imam Khomeini ya yi karatu na tsawon shekara daya a karkashin kulawar manyan malamai, Sheikh Mohammad Ali Borojerdi da Agha Sheikh Golpayegani.

Imam Khomeini bai tsaya sosai a Arak ba saboda Hajj Sheikh Abdul Karim Ha'erri Yazdi ya bar Arak ya tafi Qom domin ya zauna a can. Watanni hudu bayan tafiyar Abdul Karim, Imam Khomeini shima ya koma Qom ya zauna a can.

A karkashin kulawar Sheikh Ha'erri, ya samu kwarewa a bangarori daban-daban na karatun addinin musulunci.

Rayuwar Iyali

Imam Khomeini ya yi aure yana da shekaru 27. Ya auri 'yar Mirza Mohammad Thaqafi a shekarar 1929. Thaqafi na daya daga cikin manyan malaman Tehran. Imam Khomeini na da yara bakwai. Maza biyu, mata biyar, sunanyen 'ya 'yansa maza shine Mustafa da Ahmad. Sunayen 'ya 'yansa mata shine Seddiqa-Khanoom, Farideh, Fahimeh, Sa'eedeh da Latifeh. 'Yan 'yansa mata biyu na karshe sun rasu ne yayin da suke kanana.


Wuraren da Imam ya fi mayar da hankali


A shekarar 1928 Imam Khomeini ya fara rubuta littattafai masu yawa wadanda za a iya rabawa zuwa bangarori bakwai daban-daban wato falsafa da sufi, tauhidi, ka'idojin fikihu, da'a, tafsirin Al-Qur'ani, adabi da baiti na waka da kuma siyasa da shugabanci.

A cikin wannan satin, aka bayyana sabon tsarin littattafan da Imam Khomeini ya rubuta a cikin na'ura mai kwakwalwa a Tehran. 

An dauke shi a matsayin alamar shugaba ga kasar Iran a cikin shekarun 1970s ba kamar tsohon tsarin mulkin sarauta ba na danniya na shekaru daruruwa. Ya jagoranci Juyin-juya halin Musulunci a shekarar 1979 da ya yi sanadiyyar hambarar da Shah na Iran da ke samun goyon bayan Amurka.

Kamar a shekarun baya, musulmai sun yi tururuwa zuwa gini na musamman da kabarin Imam Khomeini ya ke a kudancin Tehran. Musulmai a kasashe da dama na tunawa da marigayin shugaban domin ya karfafa gwiwar yin wasu juyin-juya halin a fadin duniya.

Imam Khomeini ya rasu a ranar 3 ga watan Yunin shekarar 1989 yana da shekaru 87.

No comments

Powered by Blogger.