Header Ads

Tsohon ɗan majalisa Kazaure ya ba Tinubu shawara kan kuɗaɗen da suka bace


Tsohon dan majalisar wakilai, Gudaji Kazaure ya bayyana sunayen mutane 12 ga shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnatinsa domin ya bincike su domin "gano kudaden Nijeriya da suka bace."

Tsohon dan Majalisar wanda ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da ya fito a cikin shirin Brekete Family, ya yabawa gwamnatin Tinubu kan cire tallafin mai nan da nan, domin kamar yadda ya bayyana, biyan tallafin "cuwa-cuwa" ce kuma hanya ta sace albarkatun Nijeriya.

Kazaure ya kara da cewa in har gwamnatin Tinubu na so da gaske ta gano duka kudaden Nijeriya da suka bace to akwai mutanen da ya kamata su fuskanci doka.

"Shi ya sa na ke kira ga shugaban kasa, kamar yadda ya shigo din nan, ya nuna cewa ba ya da wasa. Akwai mutanen da ke cikin gwamnatin sa kuma akwai mutanen da ke taimaka masa wadanda suma suna cikin wannan badakala. Ya kamata ya rufe idanunsa." Kamar yadda tsohon dan majalisar wakilan ya bayyana, inda ya kara da cewa, "Ko ma waye ke cikin gwamnatin sa, ko waye ke kusa da shi, in an same shi (yana da hannu) cikin wannan al'amari ya dawo da kudin gwamnati ba tare da tashin hankali ba saboda haka muke shiri yanzu.

"Idan bai yi hakan ba, to tozarta. Saboda haka akwai mutane 12, zan karanto su yanzu. Mutum na farko in muna so mu dawo da tattalin arziki kuma ba da wasa mu ke ba, sai mun kama tare da binciken gwamnan babban banki (Godwin Emefiele) wanda a yanzu haka ana gudanar da bincike a kan sa.

"Na biyu shugaban EFCC (Abdulrasheed Bawa); kuma in muna binciken shugaban EFCC sai mun gayyato tsohon shugaban ta (Ibrahim) Magu, ya kawo wasu abubuwa da ya bari a ofis.

"Na uku babban manajan hukumar NNPC (kamfanin man fetur na Nijeriya; Mele Kyari). Na hudu, tsohon Ministan Shari'a, (Abubakar)Malami. Na biyar, Sabiu Tunde, wanda shine sakatare na musamman na tsohon shugaban kasa (Muhammadu) Buhari.

"Na shida akwai Muhammad Nami, shugaban FIRS (Hukumar tattara harajin cikin gida). Kuma akwai Jamoh (Bashir Yusuf) darakta janar na NIMASA (Hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta Nijeriya). Sai kuma akwai (Mohamed Bello) Koko na NPA (Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa) da kuma tsohuwar shugabar NPA, Hadiza Bala.

"Sai kuma duka mataimakan gwamnan babban banki, na yanzu, da ke aiki tare da Emefiele. Ya kamata mu gayyata tare da binciken tsohuwar ministar harkokin jin kai, Sadiya Umar Farouq.

"Sai kuma baki daya shugabannin NIBSS (tsarin biyan kudade da turawa a tsakanin bankuna na kasa), baki daya shugabannin da jami'an ICT (sadarwar) da ke wurin. Ya kamata a bincike su domin su ne za su fada maka ina ne duk caje-cajen banki da "stamp duty" (kudaden harajin da gwamnati ke sa wa akan wasu muhimman kundaye wadanda mafi yawa suka kunshi tura abubuwan da aka mallaka ko wasu kadarori) suka tafi domin daga nan ne kudade ke tafiya babban banki. Sun bude ma'ajiyar sirri, suna tura kudi ga gwambati suna tura wasu a ma'ajiyar kashin kan su.

"Shugaban kasa ya kamata ya dawo da kwamiti na. Na biyu ya bari in yi aiki da darakta janar na DSS (Hukumar tsaron farin kaya) kawai domin mutum ne mai ra'ayi kuma yana a shirye domin taimakon kasar nan." Kamar yadda ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.